Gwamnatin Najeriya ta ayyana wani dan kasar Birtaniya, Andrew Wynne (Andrew Povich ko Drew Povey), a matsayin wanda take nema ruwa a jallo kan yunkurin kifar da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Rundunar ’yan Sandan Najeriya ta ce tana gudanar da bincike na musamman kan yadda sojojin sa-kai daga kasar waje suke shiga kasar suna neman hambarar da zababbiyar gwamnatin dimokuradiyya.
Mai magana da yawun rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya sanar a ranar Litinin cewa hujjojin da kuma bayanan da suka samu daga Andrew Wynne sun tabbatar da hannunsa a yunkurin kifar da gwamnatin Najeriya.
Adejobi ya bayyana cewa Andrew Wynne ya bayar da tallafin kudade da kuma tsare-tsare zanga-zangar da aka gudanar kan tsadar rayuwa da nufin amfani da zanga-zangar wajen ganin an hambarar da gwamnaitin Najeriya.
Bugu da kari dan kasar na Birtaniya ne ya ba da umarni tare da sanya ido kan zanga-zangar yunwar da aka gudanar a fadin kasar a watan Agusta.
Jami’in ya ce binciken rundunar ya gano cewa Andrew Wynne yana zaman haya ne a gidan Labour House da ke Abuja.
Adejobi, ya ci gaba da cewa Andrew Wynne ya kama wurin haya ne da sunan bude shagon sayar da litattafai mai suna ‘Iva Valley Bookshop’.
Sannan kuma shi ne ya assasa makarantar ‘STARS of Nations Schools’ domin batar da sawu game da manufarsa.