✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Juyin Mulki: Mali da Burkina Faso sun tura sojoji Nijar

Sojojin Nijar sun yi kunnen uwar shegu da barazanar ECOWAS wadda wa'adinta ya cika

Gwamnatocin sojin kasashen Mali da Burkina Faso sun tura wakilansu domin goyon bayan sojojin Nijar da suka yi juyin mulki.

Mali da Burkin Faso sun yi hakan ne bayan cikar wa’adin da kungiyar ECOWAS ta ba wa masu sojojin Nijar su mayar da mulki ga Shugaba Mohamed Bazoum da suka hambarar.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijar ta ce a ranar Litinin ake sa ran isar wakilan na Mali da Burkina Faso a birnin Yamai.

A ranar Lahadi da wa’adin na ECOWAS ya cika ne gwamantin sojin Nijar da ta yi biris da shi, ta rufe daukacin sararin samaniyar kasar.

A halin yanzu dai hankalin duniya ya koma jiran ganin mataki na gaba da kungiyar za ta dauka.

Da farko dai ECOWAS, wadda ta ce za ta sanar da matsayinta a ranar Lahadi, ta yi barazanar daukar matakin soji a Nijar, duk da cewa manyan kasashen duniya na fatan ganin an sasanta cikin diflomasiyya.

Majalisasr Dattawan Najeriya dai ta ki amincewa da bukatar Shugaban Kasa Bola Tinubu, wanda shi ne Shugaban ECOWAS na daukar matakin soji a Nijar.

Yamutsi tsakanin Nijar da kungiyar ECOWAS mai kasashe mambobi 15 a Yammacin Afirka na iya ta’azzara matsalar da ake fama da shi a yankin na fatara da kuma rashin tsaro.

Gwamnatocin sojojin Mali da Burkina Faso da Guinea Bissau sun riga sun lashi takobin tura sojoji sa kuma yakar duk kasar da ta yi kokarin yakar takwarorinsu na Nijar. Sojoji sun yi juyin mulki a 2020 a Mali, a Burkina Faso kuma a 2022.

Sojojin na Nijar kuma sun kulla yarjejeniya da kamfanin sojojin sa-kai na Wagner na kasar Rasha, domin taimaka musu wajen yakar barazanar tsaro a kasarsu.

Sun kuma ba wa dakarun Faransa masu alaka da gwamnatin Bazoum umarnin ficewa daga kasarsu, amma Faransa ta ce allambaram, domin sojojin ba halastacciyar gwamnati ba ne.

Ana ganin yanayin tsaro da aka shiga a Nijar na iya haifar da wani rikici mai sarkakiya a yankin Sahel, ta hannun manyan kasashen duniya marasa ga-maciji da juna.

Tun a lokacin Bazoum Nijar na da sansanin sojojin Italiya da Amurka da Faransa , wadanda kuma ba sa ga-maciji da Rasha, wadda yanzu sabuwar gwamnatin sojin kasar.

A baya Faransa na da dakaru a Mali da Burkina Faso, amma bayan sojoji sun yi juyin mulki suka kore su daga kasashen, suka koma hulda da Rasha, suka kuma dauki hayar kamfanin Wagner.

Dakarun Faransa da Burkina Faso ta kora a baya-bayan nan sun koma Nijar da zama, kafin masu juyin mulkin Nijar su ba su wa’adin barin kasar.

Nijar ta kasance wa Amurka, mai babban sansanin jirage mara matuka a Nijar da Faransa, tsohuwar uwar gijiyar Nijar, babbar cibiyar a yankin Sahel, inda kasashen biyu ke kokarin samun karfin iko da gindin zama ta fuskar tsaro.

A halin yanzu da Rasha take samun gindin dama ta fuskar tsaro da tattalin arziki, hambararren shugaban kasa Bazoum na kira ga Amurka da manyan kasashen duniya su ceto kasarsa daga hannun Rasha, wadda ya suffanta da ayyukan ta’addanci.

Manyan abokan hamayyar Rasha guda biyu, Amurka da Faransa dai na magana da kakkausan lafazi a kan zuwa Rasha yankin Sahel, sai dai  kuma bisa dukkan alamu gwamantocin sojin yankin sun fi samun nutsuuwa da ita.

Amurka da Faransa da ECOWAS da Majalisar Dinkin Duniya sun janye tallafinsu ga Nijar, ko da yake, ministan harkokin wajen Italiya, Antonio Tajani, ya ce yana fata ECOWAS za ta kara wa’adin da ta ba wa sojojin na Nijar, haka kuma ba ya ganin Amurka za ta yi amfani da karfin soji a Nijar.