Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga sojoji da su saki shugabannin kasar ba tare da bata lokaci ko sharadi ba.
Ofishin Majalisar Dinkin Duniyar na kasar Mali ya kuma yi kira da a kwantar da hankali a kasar da ke fama da tashin hankali, wanda a halin yanzu ake fargabar sojojin sun yi juyin mulki.
Kiran na zuwa ne bayan rudani da rashin tabbas da aka shiga bayan sojojin sun yi awon gaba da shugaban rikon kwarya, Bah Ndaw tare da Firai Minista Moctar Ouane, da Ministan Tsaro Souleymane Doucore zuwa barikin soja na Kati da ke kusa da Bamako babban birnin kasar.
Tabarbarewar lamuran siyasa da rikici tsakanin sojoji na gurgunta kokarin da shugabanni da kasashe makwabta ke yi na kyautata halin da kasar mai fama da talauci ke ciki, wacce take kuma taka rawa wurin tabarbarewar tsaro a yankin yammacin Afirka.