Wani jirgi mallakin kamfanin jiragen sama na Max Air ya makale a filin sauka da tashin jiragen sama na Diori Hamani da ke Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar bayan juyin mulkin da aka yi a kasar.
Rahotanni sun ce jirgin, mai lamba 5N-ADM, ya sauka a Yamai ne bayan ya kwaso alhazan kasar daga kasar Saudiyya.
- Juyin Mulki: Wane ne zai zama sabon Shugaban Nijar?
- A gaggauta sakin Bazoum ba tare da bata lokaci ba — Majalisar Dinkin Duniya
Sai dai ba zai iya tashi ya bar birnin ba saboda rashin tabbas din da aka shiga, sakamakon hambarar da Shugaban Kasar, Mohammed Bazoum, da sojojin kasar suka yi a ranar Laraba.
Jirgin, a cewar rahotanni, ya sauka a Yamai ne da alhazan Najeriya su 360 wajen misalin karfe 10:40 na daren Laraba.
Muna tafe da karin bayani…