✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Juyin Mulki: Faransa ta dakatar da tallafin da take bai wa Nijar

Kungiyar Kasashen Afirka ta ba sojojin wa’adin kwana 15 su koma bariki.

Faransa ta dakatar da ilahirin gudummawar ci gaban kasa da cike gibin kasafin kudi da take bai wa Jamhuriyyar Nijar.

Wannan dai wani mataki na mayar da martani sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum a wannan makon.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Faransa ta bukaci a dawo da tsarin mulki karkashin zababben Shugaba Mohamed Bazoum.

Tun da farko Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da janyewar hadin kai a fannin tsaro da taimakon kudade tsakaninta da Nijar.

Wannan na zuwa ne bayan da Kungiyar Kasashen Afirka ta ba sojojin wa’adin kwana 15 su koma bariki.

A gobe Lahadi Shugabannin Afirka ta Yamma za su gana don tattauna batun na Nijar.

Haka kuma, a yayin ziyararsa a Papua New Guinea a ranar Juma’a, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi Allah-wadai da juyin mulkin, yana mai bayyana shi a matsayin hatsari ga yankin, sannan ya bukaci sojojin da su saki Bazoum da suke tsare da shi tun ranar Laraba.

Nijar dai, ita ce kasa ta karshe a yankin Sahel da ke ci gaba da dasawa da Faransa a daidai lokacin da yankin ke ci gaba da fama da rashin tsaro da hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi.

A farkon wannan shekarar ce, Faransa ta kawo karshen aikinta na yaki da ta’addanci a Mali tare da janye sojojinta bayan gwamnatin mulkin sojin kasar ta bukaci haka.

Yanzu haka akwai sojojin Faransa dubu 1 da 500 da ke zaune a Jamhuriyar Nijar, inda suke gudanar da aikin hadin-guiwa da takwarorinsu na kasar.

Juyin mulkin da sojojin suka yi a birnin Yamai, shi ne na uku da aka gani a yankin Sahel tun daga shekarar 2020 bayan wadanda aka gani a Mali da Burkina Faso.