✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Juyin mulki: ‘Fadar Shugaban Kasa na cikin rudani’

Fadar Shugaban Kasa na cikin zullumi kan rahoton zargin neman kifar da Gwamnatin Shugaba Buhari.

Fadar Shugaban Kasa na cikin rashin tabbas bayan bullar rahoton da ke zargin ana yunkurin kifar da Gwamnatin Shugaba Buhari.

Masanin Halayyar Dan Adam, Dokta Abubakar Umar Kari ne ya bayyana hakan, tare da cewa a halin yanzu Gwamnatin Buhari ta rasa tudun dafawa game da lamarin.

“’Yan Najeriya ba su taba fusata kamar yanzu ba inda ’yan ta’adda suke sheke ayarsu sun karkashe mutane haka kawai, ba tare da sun fuskanci wata turjiya ba.

“’Yan adawa kuma sai amfani da yanayin suke yi suna kara matsa wa gwamnatin lamba da caccaka da a wasu lokutan suke yi da kakkausar muryar, ko ma da sigar cin amanar kasa,” inji Dokta Kari.

Ya bayyana hakan ne a yayin da yake sharhi kan bayanin da Fadar Shugaban Kasar ta fitar game da zargin neman kifar da gwamnatin.

Sai dai ya ce, akwai yiwuwar Fadar Shugaban ta bayyana batun yunkurin hambarar da gwamnatin ne da nufin yi wa masu manufar kandagarki.

Babban Lauyan Najeriya, Dayo Akinlaja, ya ce doka ta ba wa shugabannin siyasa damar bayyana yanke kaunarsu daga duk wata gwamanti.

“Yana daga cikin ’yancin da doka ta bayar na samun ra’ayi da kuma bayyana su,” inji shi.

Sai dai ya yi kashedi da cewa duk taron da shugabannin siyasa za su kira a halin yanzu, wajibin ne manufarsu ta kasance tan kwantar da hankula ba su tunzura jama’a ba.