An bayar da rahoton cewa wasu mutane dauke da makamai sun yi awon gaba da jami’an gwamnatin rikon kwarya ta Sudan da dama.
Kafar yada labarai ta BBC Africa ta ruwaito cewa har gida aka bi jami’an aka tasa keyarsu, yayin da turka-turkar siyasa ke dada kazancewa a kasar ta Sudan.
- Saudiyya: Sarki Salman Ya Kara Wa’adin Zaman Baki Kyauta
- Lalata Da Dalibai: Poly Bauchi Ta Kori Malamai Daga Aiki
Wata majiya a gwamnatin ta tabbatar da faruwar lamarin ga kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, “Wasu mutane dauke da makamai sun kama shugabannin gwamnati da na siyasa da dan dama”.
An ce wasu sojoji da ba a san ko su wane ne ba sun tsare ministoci akalla hudu jim kadan da ketowar alfijir ranar Litinin.
Har yanzu dai babu tabbas a kan ko wane ne ke da alhakin kama jami’an – rundunar sojin kasar ta ki ta ce uffan a kan lamarin.
Har da Firai Minista?
Wasu rahotanni sun nuna cewa an kama Firai Minista Abdallah Hamdok, wanda farar hula ne, ko da yake ba a tabbatar da hakan ba.
BBC ta bayar da rahoton cewa babu intanet a Khartoum, babban birnin kasar, yayin da wasu hotuna da ke nuna gungun fusatattun mutane suna kona tayoyi a kan tituna suka fara karakaina a kafafen sadarwa na zamani.
AFP ya ruwaito cewa a birni na biyu mafi girma a kasar ma, wato Omdurman, an katse hanyoyin sadarwa na intanet, yayin da gidajen rediyo da talabijin ke saka wakokin kishin kasa.
Babbar kungiyar masu rajin tabbatar da dimokuradiyya a Sudan ta yi kira ga magoya bayanta su nuna turjiya ga duk wani yunkuri na “juyin mulkin soji”.
Me ya yi zafi?
Wannan lamari dai na faruwa ne kwana biyu bayan da daya daga cikin kungiyoyin kasar da ke kira da a mika mulki kacokan a hannun farar hula ta yi gargadin cewa ana “yunkurin juyin mulki”.
Kungiyar ta yi gargadin ne yayin wani taron manema labarai da wani gungun mutane da ba a san su ba suka yi yunkurin tarwatsawa.
Tun bayan hambarar da Shugaba Omar al-Bashir a watan Afrilun 2019 kasar ta Sudan ke fadi-tashin kafa sabuwar gwamnati, sai dai rikita-rikitar siyasar da fafutukar kaiwa ga madafun iko suna yi wa lamarin tarnaki.
Tun watan Agustan 2019 kasar ke karkashin jagorancin shugabancin hadin gwiwa tsakanin sojoji da farar hula wanda aka dorawa alhakin mayar da kasar turbar mulkin farar hula zalla.
Sai dai babbar hadakar jam’iyyu da kungiyoyin farar hula wadda ta jagorancin zanga-zangar nuna adawa da al-Bashir a 2019, FFC, ta dare gida biyu masu adawa da juna.
A cewar shugaban bangaren FFC mafi girma, Yasser Arman, yayin da yake jawabi ga ‘yan jarida ranar Asabar, “Wannan rikici da muka fada ciki kitsa shi aka yi, kuma yunkuri ne na juyin mulki.
“Muna jaddada goyon bayanmu ga gwamnati, da Firai Minista Abdalla Hamdok, da cibiyoyin da ke aikin kaow sauyi”.