Kungiyar Kwallon Kafa Juventus, ta cimma yarjejeniyar sakar wa Manchester United tauraronta, Cristiano Ronaldo a kan kudi yuro miliyan 15 (kwatankwacin fam miliyan 12.86 kamar yadda kungiyar ta Serie A ta sanar.
Tun a ranar Juma’ar da ta gabata ce United ta sanar da kulla yarjejeniyar dawo da dan wasanta na kasar Portugar mai shekara 36 zuwa kulob din gabanin yi masa rajista, samun takardun izini zama a Birtaniya da kuma tabbatar da koshin lafiyarsa.
- Mai shekara 100 ta zama mafi karfi wajen daga karfe a duniya
- Mahara sun kashe wani jagoran al’umma a Kwara
Cikin wata sanarwa da Juventus ta fitar saura kiris a rufe kasuwar musayar ’yan kwallo, ta tabbatar da cewa United za ta biya yuro miliyan 15 kan dan wasan da kuma yuro miliyan 8 kari a kan yarjejeniyar.
Sanarwar ta ce, “Juventus FC ta cimma yarjejeniya da Manchester United domin daukar Cristiano Ronaldo.
“A yanzu haka United ta samu tabbacin yi wa dan wasan rajista la’akari da yuro miliyan 15 da za ta biya cikin shekaru biyar.
“Wannan na iya karuwa da yuro miliyan takwas bayan cimma hakikanin manufofin da ake bukatar dan wasan ya aiwatar a tsawon lokacin da kwantaraginsa ya kayyade.”
Bayanai sun ce Ronaldo ya sanya hannu kan kwangilar shekara biyu a Old Trafford, tare da zabin tsawaita zamansa da shekara daya.
Ya ce, Manchester United kungiya ce da ke da mazauni na musamman a zuciyarsa inda ya bayyana matukar mamakin irin sakonnin da ya samu tun da aka bayar da sanarwar komawarsa a ranar Juma’a.
A cewarsa, “Na zaku na buga wasa a Old Trafford a filin da ke cike da ’yan kallo sannan na sake haduwa da magoya bayana.”
A bangaren Kocin United, Ole Gunnar Solskjaer ya ce: “Ba a iya bayyana Cristiano ba. Shi mutum ne mai girma da ban mamaki.
“Samun kwarin gwiwa da damar murza leda a babban mataki na tsawon shekaru yana bukatar mutum na musamman
“Ba na shakkar cewa zai ci gaba da burge dukkanmu kuma kwarewarsa za ta karfafa gwiwar matasan ’yan wasan kungiyar nan.
“Komowar Ronaldo ta nuna abu na musamman da kungiyar ne take da shi kuma ina matukar farin cikin ganin zai komo inda ya soma wasa.”
Alkaluma na tarihi sun tabbatar da cewa Ronaldo ya zira kwallaye 118 a wasanni 292 da ya buga wa United a zamansa na farko kafin ya tafi Real Madrid a 2009.
Ronaldo wanda ya kwashe shekaru shida yana murza leda a United, ya lashe kofuna uku na Gasar Firimiya, kofin Zakarun Turai daya, kofin Lig daya da kuma na FA daya.
Ya kuma dauki kofin Fifa Club World Cup da na Community Shield duk a karkashin jagorancin Sir Alex Ferguson.