Good Friday wato Juma’a Mai Tsarki, ko Babbar Juma’a, Rana ce da Kristoci a fadin Duniya ke tunawa da giciyewa da kuma mutuwar Yesu Almasihu a bisa kan Giciye wato (Cross), a kowacce shekara.
Ranar Juma’a Mai Tsarki, na fadowa ne a cikin Mako Mai Tsarki Wanda ake kira ‘Holy Week’ a Turance, a cikin mako na karshe na Azumin kwana 40 da Kiristoci da dama a fadin duniya suka yi.
- Isra’ila ta kai hari masallacin birnin Kudus, ta raunata masallata 158
- Amurka ta amince ta sayar wa Najeriya makaman yaki na biliyan 413
Wannan rana na da muhimmanci sosai ga kowanne Kirista a duniya, saboda kalaman da Yesu Ya furta a bisa kan Giciye kafin ya koma ga Allah.
Hakan ne ya sa ya kamata kowanne Kirista ya yi azumi, da adu’a, da kuma ba da sadaka a lokacin.
Kiristoci na wadannan ayyukan ne domin tunawa da aikin ceton da Isa Almasihu Ya yi wajen ceton dukkan ’yan Adam daga zunubansu, ta wajen mutuwarsa a bisa kan Giciye.
So da dama, a kan yi tambaya, me ya sa ake kiran ranar, Juma’a Mai kyau ko Juma’a Mai Tsarki?
Amsar ita ce, saboda Almasihu ya mutu domin zunuban ’yan Adam.
Rana ce kuma da ke shirya zuwa ranar bikin Easter, wato ranar Lahadin da ke biye mata.
Sai ku tare mu ranar Lahadin domin sanin me ya sa Kiristoci ke bikin Easter.