Tsohon Shugaban Kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan zai jagoranci taron tattaunawa na Daily Trust Dialogue na bana da za a gudanar a ranar Alhamis.
Taron wanda shi ne karo na 18 zai tattauna ne a kan maudu’in sauya tsarin Najeriya (Restructuring), wanda aka jima ana mahawara a kai a kasar.
- ’Yan sanda sun cafke mace mai garkuwa da mutane a Kano
- An kama masu hako kawunan mutane a kabari
- Za a dauki nauyin karatun gurguwar da ke rarrafen zuwa makaranta har jami’a
- Tsoron iyayenmu na hana maza neman aurenmu —’Yan matan barikin soja
Fitacciyar ‘yar jarida, Kadaria Ahmed, ce za ta jagoranci gabatar da taron wanda zai gudana a Abuja, wanda kuma zai karbi bakuncin fitattun mutane daga sassan Najeriya da za su yi jawabi kan batun.
Masu jawabin su ne masanin kimiyyar siyasa kuma tsohon Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega da dattijo kuma kusa a Kungiyar Al’ummar Yarabawa ta Afenifere, Cif Ayo Adebanjo da kuma tsohon Shugaban Kungiyar Kabilar Igbo ta Ohanaeze Nd’Igbo, Cif John Nnia Nwodo.
Taken Daily Trust Dialogue na bana zai mayar da hanakli ne kan manufar sauya tsarin Najeriya, dacewar hakan, yaushe da kuma yadda ya kamata a yi.
Za a gudanar da taron ne a dakin taro na NAF Conference Centre and Suites, da ke kan Titin Ahmadu Bello Way, Kado, Abuja, da karfe 10 na safe.
Manyan baki da za su halarci taron sun hada da shugabannin manyan kungiyoyin yankuna da kuma siyasa a Najeriya da suka hada da Majalisar Sarakunan Najeriya (NCTRN), Gammayyar Kungiyoyin Mata ta Najeriya (NCWS), da Majalisar Matasan Najeriya (NYCN).
Akwai kuma Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF), Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), Kungiyar Afenifere, Kungiyar Ohanaeze Nd’Igbo da Kungiyar Al’ummar Yankin Arewa ta Tsakiya (NCPF), da sauransu.
Manyan mutane da za su halarci taron sun hada da gwamnoni, ministoci, ‘yan majalisa tsoffi da masu ci.
Akwai kuma shugabannin jam’iyyun siyasa, kungiyoyin kare hakki, kungiyoyin kasashe da kuma jakadun kasashe.
Sanarwar da Mukaddashin Shugaban Kamfanin Daily Trust, masu buga jaridar Daily Trust da Aminiya da sauransu, Nura Mamman Daura, ya fitar ta ce, “sabanin tarukan da aka yi a baya, na bana za a halarta ne a zahiri da kuma ta bidiyo saboda dokokin takaita cudanyar mutane sakamkon annobar COVID-19”.
Ya ce mutun 50 da suka hada da Shugaban taron, mai gabatarwa da masu jawabi da wasu manyan baki za su hallara ne a zauren taron, sauran manyan baki da mahalarta kuma ana gayyatar su da su yi amfani da adireshin nan na webinar don halarta daga duk inda suke ta bidiyo: https://zoom.us/webinar/register/WN_b-W7SigrTu-nQq4XY8-QWw.
Za kuma a yada taron kai tsaye a talabijin ta tashohin kawayen masu shirya taron da suka hada da Arise TV (DSTV Channel 416; GoTV Channel 44; Sky Channel 519; Freeview Channel 136); AIT (DSTV Channel 253; GoTV Channel 93; Sky Channel 454; da kuma StarTimes Channel 494.
Za kuma a rika nunawa kai tsaye a intanet ta shafin Trust TV da shafukan zumunta na Daily Trust.
Taron na Daily Trust Dialogue gudunmuwa ce ta kamfanin Media Trust Limited domin samar wa ‘yan Najeriya da ma Afirka fagen tattaunawa kan al’amuran da suka shafi kasa, da hadin kan Afirka domin samun cigaba ta fuskar siyasa da tattalin arziki a Najeriya da ma nahiyar Afirka.
Tun shekarar 2002 Media Trust ke gabatar da taron a duk shekara inda ake tattauna muhimman batutuwan siyasa da shugabanci.
A tsawon lokacin, taron ya samu halarcin shugabannin gwamnatoci, na Majalisar Tarayya da kwararru a fannin kasuwanci, masana’antu da kuma jakadun kasashe.
Daily Trust Dialogue ya kuma samu halarcin fitattun mutane da shugabanni daga fadin Afirka.
Daga ciki akwai tsohon Shugaban Kasar Botswana Festus Mogae, tsohon Shugaban Kasar Ghana, Jerry Rawlings, da Dokta Salim Ahmed Salim, Tshohon Fira Ministan Tanzania.
Marigayiya Winnie Mandela tsohuwar matar tsohon Shugaban Afirka ta Kudu, Nelson Mandela; Dr. Mo Ibrahim; da Misis Samia Nkrumah, ‘yar Dokta Kwame Nkrumah na daga cikin wadanda suka taba halartar taron.