✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jonathan zai iya sake tsayawa takarar Shugaban Kasa a 2023 — Kotu

Kotu ta bai wa Jonathan damar sake yin takarar a babban zaben 2023

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa, ta wanke tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan tare da cewa yana da damar yin takarar Shugaban Kasa a 2023.

Kotun ta yanke hukuncin ne ana saura kasa da sa’o’i 48 na zaben fid da gwanin Shugaban Kasa na jam’iyyar APC mai mulki.

A baya, an alakanta Jonathan da neman sake tsayawa takarar Shugaban Kasa a APC, yayin da wata kungiya ta siya masa fom kan kudi Naira miliyan 100.

Sai dai an yi ta tirka-tirka kan halaccin tsayawarsa takara a babban zaben 2023 da ke karatowa.

Sai dai a ranar Juma’a, kotun ta ce Jonathan, wanda ya fadi zaben 2015 a hannun Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, zai iya tsayawa takarar kujerar shugabancin kasar nan.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Isa Hamma Dashen ne, ya yanke hukuncin a ranar Juma’a, inda ya ce Jonathan na da ‘yancin tsayawa takarar shugabancin kasa a 2023, kuma babu wata doka da za ta iya hana shi.

A wani sammaci da Andy Solomon da Idibiye Abraham suka shigar gaban kotun, sun bukaci kotu ta bayar da umarnin hana Jonathan takara saboda ya taba yin mataimakin Shugaban Kasa, sannan ya karasa wa’adin tsohon Shugaba Umaru Musa ’Yar’aduwa.

A cikin karar, an jera sunan APC, Jonathan da kuma Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a matsayin wadanda ake tuhuma a karar mai lamba FHC/YNG/CS/86/2022 da ke gaban Mai Shari’a Isa Dashen.