✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

John Terry ya zama Mataimakin Kocin Aston Billa

Kulob din Aston Billa da ke Ingila ya bayar da sanarwar nada sababbin manajoji. Sanarwar ta nuna an zabi Dean Smith a matsayin sabon koci…

Kulob din Aston Billa da ke Ingila ya bayar da sanarwar nada sababbin manajoji.

Sanarwar ta nuna an zabi Dean Smith a matsayin sabon koci yayin da aka zabi tsohon dan kwallon Chelsea John Terry a matsayin mataaimakinsa.  Sannan kulob din ya zabi Jesus Garcia Piterach a matsayin Daraktan kula da harkokin wasanni.

John Terry ya taba buga wa kulob din Aston Billa kwallo kafin ya canza sheka zuwa kulob din Chelsea.  A kwanakin baya ne ya bayyana sanarwar daina yin kwallo da hakan ya ba kulob din Billa damar daukarsa a matsayin mataimakin koci.

Ana sa ran John Terry zai yi amfani da kwarewa wajen farfado da martabar kulob din Aston Billa da ke buga gasar rukunin ’yan dagaji a Ingila da aka fi sani da (Championship).