A karshe dai an sako wani fursuna da ya kare kusan daukacin rayuwarsa a kurukuku. Fursunan mai suna Joe Ligon ya shafe shekara dai-dai har 68 a gidan yari.
A yanzu Joe yana da shekara 82 wato an daure shi a kurukuku tun yana da shekara 14 a duniya, kuma hakan ya nuna cewa shi ne fursunan mafi tsufa a Amurka.
“Muna lalata rayuwar wadansu ta hanyar daure fursunoni fiye da kima, sannan ana bata kudi ta hanyar kara adadin kwanakin daure fursunoni.
Daurin da aka yi wa Joe na nuna wawanci ne,” inji lauyan da ya tsaya masa a karkashin Kungiyar Defender Association of Philadelphia, Mista Bradley Bridge, kamar yadda ya bayyana wa kafar labarai ta The Philadephia Inquirer da ke Amurka.
Bradley Bridge ya fara tsayawa wa Joe tun a shekarar 2006.
A safiyar Alhamis da ta gabata ce, Lauyan ya dauki Joe daga gidan kurukukun State Correctional Institution Phoenix da ke yankin Montgomery zuwa sabon gidansa.
An daure Joe Ligon ne yana saurayi a 1950, lokacin duniya tana cikin tashin hankali, saboda nuna wariyar launin fata.
Kafin shari’ar fegi ta Brown da Board of Education a 1954, wadda aka bayyana bambancin launin fata a makarantun gwamnati bai cikin tsarin kundin mulkin kasar, kuma ba a amince da shi ba.
Sanadiyyar habakar talauci da rashin aikin yi, an dakatar da gine-gine da kuma bambancin launin fata.
Joe Ligon ya tsinci kansa a cikin halin rashin sa’a da mummunan yanayi.
An samu Joe da hannu a laifuffukan fashi da kai wa wadansu harin da ya yi sanadin mutuwar mutum biyu.
“Ina kallon duk dogayen gineginen da aka yi ban san da su ba kafin in zama fursuna,” inji Joe Ligon.
“Duk wadannan sababbin ne a wurina kuma babu su a baya kafin in shiga gidan yari, ba a yi su ba.”
Zaman Joe Ligon a gidan yari hukuncin kotun koli ne da ta yanke masa zaman gidan yari har karshen rayuwarsa.
Sai dai kasancewar yanke wa yaro hukuncin daurin rai-da-rai sabon abu ne mai kama da mugunta, sai kotun bayan zartar da hukuncin daurin rai-da-rai ta ba shi dama don samun sassauci wanda Joe Ligon ya ki amincewa da hakan.