✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jirgin yakin sojoji ya hallaka masunta 20 a Borno ‘bisa kuskure’

Harin na zuwa ne kasa da mako biyu bayan makamancin wannan harin a Yobe.

Akalla masunta 20 ne jirgin yakin sojojin Najeriya ya hallaka yayin wani ruwan wuta a garin Kwatar Daban Masara da ke Jihar Borno.

Wasu majiyoyi daga jami’an tsaro a yankin ne suka tabbatar wa da Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP) da faruwar lamarin.

Da safiyar ranar Litinin ne dai jirgin yakin ya kai hari garin da ke yankin Tafkin Chadi wanda ya hada iyakar kasahen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi.

Ana dai ganin yankin a matsayin wani sansanin mayakan kungiyar ISWAP.

Rahoton na zuwa ne kasa da mako biyu bayan makamancin wannan harin na sojojin ya hallaka mutum tara a wani kauye da ke Jihar Yobe.

A kwanan nan ne dai kungiyar ISWAP ta dage haramcin da ta sanya wa masunta a yankin, inda ta kyale su su ci gaba da gudanar da sana’arsu ta Su ba tare da tarnaki ba, lamarin da ya sa suka fara dawowa bayan sun kaurace a baya.

“Duk masuncin da ya je wannan yankin to yana jefa rayuwarsa ne cikin hatsari, saboda ba za a iya banbance shi daga ’yan ta’adda ba a yankin,” inji wani mazaunin yankin.

“Daga bayanan da muka tattara, mutanen da suka mutu za su haura 20.”

Wani masunci a yankin, Labo Sani, ya shaida wa AFP ta wayar salula cewa jirgin ya kai harin ne garin Kwatar Daban Masara da misalin karfe 6:00 na safe, inda ya kashe kusan masunta 20.

Kazalika, shi ma wani masunci a yankin, Sallau Arzika ya ce, “Jirgin ya yi ruwan wuta ne a kauyenmu, sannan ya kashe mana mutane da dama lokacin da suke kamun kifi.

“Da farko dai mutanen da suka mutu sun kai 20, amma daga bisani adadin ya karu saboda wadanda suka sami raunuka sun ci gaba da mutuwa,” inji shi.

Labarin harin dai ya yi jinkirin fitowa ne saboda karancin hanyoyin sadarwa a yankin.

Sai dai ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, kakakin Rundunar Sojin Saman Najeriya bai amsa kiran wayar da aka yi masa don neman karin bayani a kan harin ba.