’Yan ta’adda da dama sun mutu bayan luguden wuta da jirgin yakin sojin saman Najeriya ya yi musu a hananan hukumomin Birnin Gwari da Chikun a Jihar Kaduna.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan, ya ce jami’an tsaro sun bayyana wa gwamnatin jihar yadda suka samu nasarar kashe ’yan ta’addan.
- An Cafke ’Yan IPOB Da Suka Kai Hari Ofishin INEC A Imo
- Zan kawo karshen ’yan bindiga cikin kankanin lokaci —Tinubu
Ya ce, “An lalalta wani sansanin ’yan ta’adda da makaman roka a yankin Kofita da Dajin Kuyanbana da ke Birnin Gwari.”
A cewar Aruwan, jami’an tsaron sun kuma lalata wani sansanin ’yan ta’adda da ke yankin Kasarami a Karamar Hukumar Chikun.
Sun kuma lalata gidan wani kasurgumin dan bindiga mai suna Alhaji Lawan, sai dai bai yi cikakken bayani ko an kashe dan bindigar ba.
Sansanin ’yan ta’adda da dama sun lalace bayan ruwan wuta babu kakkautawa da sojin saman Najeriya ke ci gaba da yi ba dare, ba rana.
Sanarwar ta ce, “jiragen yaki na ci gaba da kai samame yayin da sojojin ke fatattakar ’yan ta’adda a yankin,” in ji sanarwar.
A halin da ake ciki, Aruwan, ya ce dakarun soji na ci gaba da tsaron titin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja don bai wa fasinjoji kwanciyar hankali yayin tafiya.