✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun harbo jirgin yaki a Zamfara

Matukin jirgin ya tsallake rijiya da baya bayan ’yan bindiga sun harbo jirgin.

’Yan bidinga sun harbo jirgin yakin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya a Jihar Zamfara.

Kakakin Rundunar, Edward Gabkwet, ya ce jirgin samfurin Alpha Jet ya rikito ne bayan ’yan bindiga sun bude masa wuta a tsakanin  iyakar jihohin Zamfara da Kaduna a ranar Lahadi.

Ya tabbatar wa ’yan jarida a ranar Litinin cewa, “Ta hanyar amfani da tunaninsa na tsira, matukin jirgin, wanda ya gamu da mummunar hari daga ’yan binidga, ya kauce musu ya nemi mafaka a garuruwan da ke kusa har zuwa faduwar rana”.

Ya ce daga bayan an kubutar da matukin jirgin, Flight Lieutenant Abayomi Dairo, wanda ya yi saukar lema daga jirgin da aka kai wa harin.

Jami’in ya ce bayan yin saukar lema, matukin jirgin ya yi ta sanda yana kauce wa mafakan ’yan bindiga har ya isa sansanin Rundunar Sojin Kasa.

A ranar Lahadin wasu labarai suka bayyana game da faduwar wani jirgin soji, amma daga baya Rundunar Sojin ta karyata labarin.

Harin na ranar Lahadi shi ne na biyu da abokan gaba suka harbo jirgin soji a 2021 —kodayake ana takaddama kan ikirarin kungiyar Boko Haram na harbo na farkon a Jihar Borno.

Karo na hudu kuma ke nan da jiragen sojin Najeriya suka yi hatsari a 2021.

Kafin na ranar Lahadi, a watan Mayu, hatsain jirgin soji, wanda shi ne na ukun a shekarar, ya ritsa da tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar-Janar Ibrahim Attahiru da ’yan tawagarsa a watan mayu.