✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jirgin yaki ya hallaka shugaban ’yan bindiga a Kaduna

Madugun ’yan bindiga, Rufa’i Maikaji da yaransa fiye da 10 sun bakunci lahira a harin.

Wani madugun ’yan bindiga, Rufa’i Maikaji da yaransa sun bakunci lahira bayan jiragen soji sun yi musus luguden wuta a Jihar Kaduna.

Gwamnatin Jihar ta ce an bindige shugaban yan bindigar tare da yaransa fiye da 10 ne a yankin dajin Falul lokacin da suke kokarin tserewa.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gidan Jihar, Samuel Aruwan, ya ce an yi wa tawagar yan bindigar ruwan wutar ce, a yayin da suke neman sulalewa da suka hangi dakarun soji, jim kadan bayan sun kai hari.

Aruwan ya ce yan bindiga sun kai harin ne a kauyen Anaba da ke Karamar Hukumar Igabi inda suka kona gidaje tare da yin garkuwa da wasu mutane.