Wani madugun ’yan bindiga, Rufa’i Maikaji da yaransa sun bakunci lahira bayan jiragen soji sun yi musus luguden wuta a Jihar Kaduna.
Gwamnatin Jihar ta ce an bindige shugaban ’yan bindigar tare da yaransa fiye da 10 ne a yankin dajin Falul lokacin da suke kokarin tserewa.
- Matawalle ya fara bayyana masu hannu a sace daliban Jangebe
- ’Yan bindiga sun kai hari Kano
- Ba za mu lamunci haramta tashi da saukar jirage a Zamfara ba — Majalisar Dokoki
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gidan Jihar, Samuel Aruwan, ya ce an yi wa tawagar ’yan bindigar ruwan wutar ce, a yayin da suke neman sulalewa da suka hangi dakarun soji, jim kadan bayan sun kai hari.
Aruwan ya ce ’yan bindiga sun kai harin ne a kauyen Anaba da ke Karamar Hukumar Igabi inda suka kona gidaje tare da yin garkuwa da wasu mutane.