✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jirgin yaki da Boko Haram ya bace a Borno

Ba a san inda jirgin ya shiga ko musabbabin katsewar layin sadarwarsa ba

Wani jirgin yakin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta aka tura yaki da Boko Haram ya bace.

Jirjin yakin, samfurin Alpha, an daina jin duriyarsa ne a yayin da yake rufa wa sojin kasa baya a lokacin da suke fatattakar Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas.

“An daina samun bayanai daga jirgin da misalin 5:08 na yamma, ranar 31 ga Maris, 2021.

“Babu cikakkun bayanai game da inda jirgin ya shiga ko musabbabin katsewar layin sadarwarsa, amma nan gaba za mu sanar da mutane da zarar an samu bayanan,” inji Daraktan Yada Labaran Rundunar, Commodore Edward Gabkwet, a cikin wata sanarwa.

A halin yanzu dai Rundunar Tsaron Najeriya ta dukufa wajen ganin an gona jirgin da kuma ceto matukansa.