Wani jirgin sama mallakar rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF) ya yi hatsari a Jihar Neja.
Jirgin wanda tsautsayin ya rutsa da shi a wannan Litinin din na kan hanyar zuwa Kadune ne daga ta jihar ta Neja.
- Dalibai mata 5 da aka sace a Jami’ar Zamfara sun shaki iskar ’yanci
- An dora mutum 8,000 kan maganin tarin fuka cikin mako daya a Kano
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar sojin saman, Air Commodore Edward Gabkwetnin, ya ce jirgin mai saukar angulu samfurin MI-171, ya fadi ne da misalin karfe 1.00 na rana a Kauyen Chukuba da ke Karamar Hukumar Shiroro a Neja.
A yayin da ake ci gaba da kokarin kubutar da fasinjojin jirgin, Mista Gabkwetnin ya ce tuni bincike ya kankama domin gano musabbabin faruwar lamarin.