✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dora mutum 8,000 kan maganin tarin fuka cikin mako daya a Kano

Gwamnatin jihar ta ce wannan shi ne adadin mafi girma da aka taba samu a Najeriya.

Gwamnatin Jihar Kano ta ce an dora mutum 8,277 a kan maganin cutar tarin fuka a cikin mako guda da ya gabata.

Gwamnatin ta ce wannan shi ne adadi mafi girma da aka taba samu a duk shekara a Najeriya.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a wajen taron makon gwajin tarin fuka na kasa na 2023, a ranar Litinin.

Ya ce, “Kano ce jiha mafi yawan al’umma a Najeriya kuma daya daga cikin jihohi biyar masu fama da cutar tarin fuka, inda a yanzu adadin masu dauke da tarin fuka ya kai 34,547.

“Ina mai farin cikin sanar da ku cewa a makon da ya wuce mun dora mutum 8,637 a kan magani.

“Mun samu jimullar masu fama da cutar tarin fuka 8,277 wanda ke nuna kashi 96 cikin 100 da aka dora a kan magani, wanda shi ne adadi mafi girma da aka taba samu a duk wata a Najeriya.

“Najeriya ce ta daya a Afirka kuma ta shida a duniya a cikin kasashe 30 da ke fama da cutar tarin fuka.

“A cewar rahoton 2022 na duniya na tarin fuka, an ceto rayuka sama da 72,000,000 tsakanin shekarar 2000 zuwa 2021 ta hanyar hadin gwiwa don kawo karshen tarin fuka a duniya.

“Har ila yau, daga rahoton, adadin mutanen da suka kamu da cutar a duniya ya kai miliyan 10.6, inda mutane miliyan 1.6 suka mutu ciki har da mutane 218,000 da ke dauke da cutar kanjamau a duniya baki daya.”