✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna asarar N13bn duk mako saboda rufe iyakar Najeriya da Nijar – ’Yan kasuwa

Sun roki Tinubu ya bude su saboda asarar da suke tafkawa

’Yan kasuwar Arewacin Najeriya sun koka da cewa suna tafka asarar sama da Naira biliyan 13 duk mako saboda rufe iyakokin Najeriya da Nijar sanadiyyar rikicin kasar.

A ranar 4 ga watan Agusta, Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ba hukumar Kwastam umarnin rufe dukkan iyakokin kasar da Jamhuriyar Nijar.

Iyakokin sun hada da ta Jibiya da ke Jihar Katsina da ta Illelah a Jihar Sakkwato da kuma ta Maigatari a Jihar Jigawa.

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja ranar Lahadi, Shugaban kungiyar ’yan kasuwa na Arewacin Najeriya, Ibrahim Yahaya Dandakata, ya ce matakan da aka dauka sun jefa su cikin tsaka mai wuya.

Sai dai ya yi kira ga Gwamnatin Najeriya da ta taimaka ta bude iyakar Maje-Illo da ke Jihar Kebbi, domin ta ba su damar shigo da kayayyaki cikin kasa.

A cewarsa, “Tun bayan umarni Shugaban Kasa kan rufe dukkan iyakokin Najeriya da Nijar sakamakon juyin mulkin da aka yi a can, muke cikin tsaka mai wuya. ’Yan kasuwar Arewa na tafka asar Naira biliyan 13 kowanne mako.

“Galibi cinikayyar da ake yi tsakanin Najeriya da Nijar gwamnati ma ba ta da kididdigarta, ko a bara ta kayan marmari ta kai kusan biliyan 177 na kayayyaki irin su dabbobi da kayan amfanin gona.

“Saboda haka, ci gaba da rufe wadannan iyakokin zai yi mummunar illa ga ’yan kasuwar kasashen biyu,” in ji shi.

Shi ma da yake jawabi, wani dan kasuwar mai suna Hamza Saleh Jibiya, ya ce tun rufe iyakokin, sama da manyan motoci 2,000 ne da ke makare da kayan da za su iya lalacewa suke can a tsaye ba damar wucewa.

“Tsaka-tsakin kwantaina tana kamawa daga tsakanin Dala 20,000 zuwa 70,000, wanda a kiyasinmu za su kai kusan Naira miliyan 140, wadanda a yanzu haka suna can a tsaye cak,” in ji shi.