Wani jirgin saman rundunar sojojin saman Najeriya NAF ya yi hatsari a Makurdi, babban birnin Jihar Benuwe.
Bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru ne da Yammacin ranar Juma’a, yayin da ake wani aikin horo a cikin jirgin na FT-7NI.
Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, Air Commodore Edward Gabkwet ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
Ya ce matukan jirgi biyu na samun kulawa a asibitin sojojin sama da ke brinin Makurdi.
“An yi sa’a, matukan jirgin biyu da ke cikin jirgin sun tsira daga hatsarin bayan da suka yi nasarar ficewa daga cikin jirgin.
“Bugu da kari, babu asarar rayuka ko asarar dukiya a inda hatsarin ya faru.
Ya kara da cewa a halin da ake ciki, babban hafsan sojin sama na Najeriya, Air Vice Marshal Hassan Abubakar, ya kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin hatsarin nan take.