Wani jirgin sojin Najeriya ya jefa wa fararen hula bom inda ya kashe fararen hula bakwai a yankin Yani da ke Ƙaramar Hukumar Safana ta Jihar Katsina.
Mamatan sun hada da mutum shida ’yan gida ɗaya, kamar yadda wani shaida ya bayyana.
Hakan na zuwa ne bayan wasu jami’an tsaro da suka hada da ’yan sanda biyu da wani jami’in Rundunar Tsaron Al’umma na jihar (CWC) sun kwanta dama a yayin musayar wuta da ’yan bindiga a Ƙaramar Hukumar a ranar Asabar.
Wani mazaunin Gundumar Zakka da ke Ƙaramar Hukumar, yankin da abin ya faru, ya bayyana cewa an yi arangamar ne bayan zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a jihar ranar Asabar, inda ’yan bindiga suka shirya kai wa masu zaɓe hari a kauyen Zakka.
Bayan samun rahoton shirin harin ne jami’an tsaron suka je domin daƙile ’yan bindigar, inda a garin haka aka yi musayar wuta tsakanin bangarorin. Wani hafsan dan sanda da jami’in CWC sun rasu, daga bisani wani ɗan sanda da ya ji rauni a arangamar ya cika.
Ya bayyana cewa, “bayan nan ne wani jirgin soji ya zo, watakila domin kai wa jami’an tsaron ɗauki. A nan ne ya jefa bom a yankin Yani da ke ƙauyen Zakka, wanda ya halaka mutum shida ’yan gida ɗaya, ya kuma jikkata wata mata.”
Wannan ba shi ne karon farko ba da jirgin soji ya kai wa fararen hula hari ba a Ƙaramar Hukumar ta Safana.
A watan Yulin shekara ta 2022 wani jirgin soji ya jefa bom a yankin Kunkumi da ke Ƙaramar Hukumar ta Safana, inda ya kashe aƙalla mutum biyu tare da jikkata wasu tara.
Wakilinmu ya yi duk ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sanda da sojoji da ke jihar game da lamarin, amma hakan ya faskara.
Amma dai kafar yaɗa labarai 4 Deutsche Welle (DW) ta ruwaito labarin harin, tana mai ambato wasu shaidu da suka tabbatar da aukuwarsa.