✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jirgin sojin sama ya yi hatsari a Kaduna

Ana fargabar matuka jirgin su biyu sun rasu a hatsarin na ranar Talata.

Wasu hafsoshin soja sun rasu a wani hatsarin jirgin soja da ya ritsa da su a Jihar Kaduna a yammacin ranar Talata.

Majiya mai tushe ta ce matuka jirgin su biyu sun rasu ne a lokacin da suke samun horo a sansanin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya da ke Kaduna.

“Abin takaici ne yadda muka rasa wasu jajirtattun hafsoshinmu biyu, Allah Ya jikan su,” a cewar majiyar mai tushe.

Mun yi kokarin samun karin bayani daga kakakin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet, saboda mun kasa samun shi a waya.

Hatsarin jirgin ya faru ne kimanin shekara guda bayan wani makamancinsa da ya ritsa wasu manyan hafsojin sojin kasa a watan Mayun 2021 a Jihar Kaduna.

Hatsarin na 2021 ya yi ajalin manyan hafsoshin sojin kasa 11, ciki har da Babban Hafsan Sojin Kasa, marigayi Manjo Janar Ibarhim Attahiru, a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa halartar taron yaye kuratan sojoji a Zariya.