✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin kasan Japan ya kafa tarihin tafiyar Kilomita 603 a sa’a 1

A ranar Talatar da ta gabata ne kasar Japan ta kafa tarihi bayan kammala gwajin wani jirgin kasa wanda ya yi tafiyar Kilomita 603 a…

A ranar Talatar da ta gabata ne kasar Japan ta kafa tarihi bayan kammala gwajin wani jirgin kasa wanda ya yi tafiyar Kilomita 603 a cikin sa’a guda kacal. Jirgin ya doke wani irinsa wanda ke tafiyar Kilomita 590 a sa’a guda. 

Sabon jirgin kasan mai suna Magleb yana amafani da wutar lantanki ne. Kuma kamfanin Central Japan Railway (JR Central) ya kera shi. Kamfanin ya ce jirgin zai fara zirga-zirga ne tsakanin birnin Tokyo da birnin Nagoya nan da shekarar 2027.
Magleb zai yi tafiyar Kilomita 280 a cikin minti 40, kasa da rabin lokacin da jirgin kasa mai gudu yake yi a halin yanzu. Kodayake, fasinjojin jirgin ba za su mori wannan gudun nasa ba, saboda kamfanin ya ce jirgin zai dinga tafiya ne kan n Kilomita 505 a kowace sa’a. Hakan na nufin jirgin ba zai dinga kure gudunsa ba.
An kera jirgin ne akan dalar Amurka biliyan 100 (kimanin naira triliyon daya ke nan), kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayyana. Zuwa shekarar 2045, ana sa ran cewa jirgin zai dangana zuwa birnin Osaka daga Tokyo a tsawon sa’a guda, madadin sa’o’i biyu da jirgin kasa ya saba yi.
Kimanin mutum 200 ne suka yi dafifi akan hanyar jirgin domin kashe kwarkwatar idonsu lokacin gwajinsa ranar Talata. “Na ji dadi matuka. Ina sha’awar shiga jirgin… Ni ma na shaida wannan sabon babin tarihin da aka shiga,” inji wata mata.
Wani jami’in kamfanin da ya kera jirgin Yasukazu Endo ya ce: “Jirgin yana kara gudu, ya kara daidaituwa akan dogonsa. Ina ganin ingancin tafiyar ta bunkasa.”