✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a bude jirgin kasa daga Abuja-Kaduna ranar Laraba

Bayan duk awa daya jirgin kasa zai rika tashi, farawa daga 29 ga watan Yuli, 2020.

Za a bude harkokin sufurin jiragen kasa da ke zirga-zirga tsakanin Abuja da Kaduna daga ranar Laraba 29 ga watan Yuli, 2020.

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Kasa (NRC) ta ce Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya sanar da cewa bayan bude tashoshin, jirgin kasa zai rika tashi a duk bayan awa daya a kowane bangare na layin jirngin kasar.

Ya ce, “Mun fuskanci matsin lamba cewa a bude tashar jirgin ganin cewa bukukuwan Sallah na matsowa”, lamarin da ake dangantawa da karuwar matsalar rashin tsaro a jihar Kaduna.

Ya sanar da haka ne a ranar Asabar a lokacin da ake yin gwajin sabbin taragon jiragen kasa a kan layin na Abuja zuwa Kaduna.

Hakan na zuwa ne mako guda bayan ministan ya sanar cewa kudin tikitin jirgin kasa zai ninku ida aka bude tashoshin.

A mako jiya ministan ya ce karin zai auku ne saboda takaita adadin fasinjoji zuwa rabi domin tabbatar da bayar da tazara a yanayin cutar coronavirus.

Ya kuma ce idan aka bude tashoshin, wajibi kowane fasinja ya mallaki sunadarin wanke hannunsa, ya kuma kasance sanye da takunkumi a tsawon tafiyar.