Mayakan Taliban a Afghanistan sun karbe iko gaba daya da filin jirgin saman Kabul ranar Talata bayan da jirgin da ke dauke da rukuni na karshe na dakarun Amurka ya bar kasar.
Hakan dai ya kawo karshen yakin da aka shafe shekara 20 ana fafatawa, kuma alamu na nuna cewa Amurka ta tafi ta bar kungiyar na da karfi fiye da lokacin da ta shiga kasar a 2001.
- Mai shekara 100 ta zama mafi karfi wajen daga karfe a duniya
- ’Yan sanda sun ceto mutum 8 daga hannun masu garkuwa a Zamfara
An dai ji karar harbe-harben bindigogi na murna a birnin Kabul, yayin da wani bidiyo ya nuna mayakan kungiyar suna shiga filin jirgin saman kasa da kasa na Hamid Karzai bayan jirgin karshe na dakarun Amurka ya bar kasar da tsakar dare.
Kakakin kungiyar, Zabihullah Mujahid ya shaida wa manema labarai a filin jirgin cewa tashin jirgin wata rana ce mai cike da tarihi a wajensu.
“Muna alfahari da wannan ranar da muka ’yanto kasarmu daga masu mamaya.
“Dubban ’yan Afghanistan ne suka gudu saboda tsoron ramuwar gayya. Sama da mutum 123,000 ne kuma sojojin Amurka suka kwashe daga Kabul a wani yanayi mai cike da hayaniya a cikin mako biyun da suka gabata,” inji Zabihullah.
Sai dai ya ce har yanzu akwai dubban mutanen da suka taimakawa kasashen Yamma da aka bari a kasar.
Sakataren Tsaron Amurka, Anthony Blinken ya ce akwai sauran Amurkawa kimanin 200 da suka so barin kasar amma suka gaza yin haka sakamakon cikar da jirgin karshen ya yi.
A cikin wata sanarwa dai, Shugaban Amurka, Joe Biden ya kare matakin gwamnatinsa na tsayawa kai da fata a kan wa’adin janye dakarun kasarsa daga Afghanistan na ranar Talata.
Ya ce yanzu haka duniya za ta zuba ido ta ga yadda kamun ludayin Taliban zai kasance bayan ta kama mulkin kasar.
“Yanzu dai mun kawo karshen zaman dakarunmu a Afghanistan,” inji Shugaba Biden, wanda kuma ya gode wa sojojin kasar saboda yadda suka kwaso mutane duk kuwa da hatsarin da hakan ke kunshe a ciki.
Hakan dai na nufin kowanne lokaci daga yanzu, Taliban za ta sanar da kafa sabuwar gwamnati a kasar. (NAN)