Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce ta ragargaza kwamandojin kungiyar Boko Haram da sansaninsu a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin kasar.
Kwadinatan Rudunar na bangaren watsa labarai, Manjo Janar John Enenche ya ce jirgin yakin ya yi luguden wuta a kebabben mazaunin jagororin Boko Haram da sauran wuraren da ke zagaye da shi.
Sanarwar da ya fitar a ranar Juma’a ta ce an kai farmakin ne ranar 17 ga watan Yuni bayan an dade ana tattara bayanan sirri da leken asirin matattarar ‘yan kungiyar.
- Sojoji sun kashe ‘yan Boko Haram 20
- Boko Haram ta yi wa fararen hula yankan rago
- Yadda Boko Haram ta zama masana’anta —Ahmad Lawan
Enenche ya ce, a yayin leken asiri da rundunar ta gudanar ta gano dandazon ‘yan Boko Haram da sansaninsu da kuma wani gida da ake tsammanin daga nan suke shirya ta’adancinsu a yankin.
Ya kara da cewa jirgin yakin sojin saman Najeriya na “Operation Long Reach”, na dakile shugabannin Boko Haram a Arewa maso gabas ne ya yi luguden wuta a wuri inda ya ragargaza maboyar ‘yan kungiyar.