Wasu sojojin Nejariya sun kwanta dama, bayan jirgin yakin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ya yi wa dakarun sojin kasa luguden bama-bamai a yankin Mainok na Jihar Borno.
Majiyarmu ta ce jirgin yakin ya bude wa sojojin wuta ne bisa kuskure, da zaton cewa mayakan kungiyar Boko Haram ne a lokacin da ayarin motocin sojojin suke kan hanyarsu ta kai dauki a yankin.
- Harin Geidam: Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 21
- Hada-hadar kudaden Cryptocurrency haramun ce —Sheik Bin Usman
Rahotanni sun ce akalla soja 30 ne suka rasu sakamakon a harin jirgin, wasunsu kuma a yayin gwabza fada da mayakan Boko Haram.
Majiyarmu ta soji ta kara da cewa harin jirgin ya kuma yi sanadiyyar asarar kayan yaki da motocin sojojin.
Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari da nufin mamaye sansanin soji a garin Mainok, inda suka gallabi dakarun, har sojojin suka bukaci a kawo musu karin dakaru.
Wani babban jami’in Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, ya shaida wa wakilinmu a sirrance cewa an tura motocin ne domin bayar da gudunmawa ga dakarun da ke Mainok, kafin jiragen su yi musu ruwan bama-bamai saboda kuskuren bayan sirrin da aka tattara.
Rundunar Sojin Sama tana bincike
Tuni dai bidiyon lamarin yake ta tashe a shafukan sada zumunta.
Mun tuntubi kakakin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Edward Gabkwet, amma ya ce shi ma ya ga bidiyon amma ba su kai ga tantance sahihancinsa ba tukutan.
Ya ce duk da haka, Rundunar ta fara gudanar da bincike domin tabbatar da hakikanin lamarin.
Ya ce, “Da farko sai mun tabbatar da ingancin bidiyon,” ya ci gaba da cewa, “Ba zai yiwu mu rika zumudin yin magana ba duk lokacin da wani bidiyo ya bulla a kafafen sada zumunta.
“Dole sai mun tabbatar da ingancinsa tukuna. Idan ya tabbata sahihi ne, sai mu yi bincike a kan abin da ya faru. Haka ake yi.
“Amma ba zai yiwu bayan na kalli bidiyon in ce kaza ne ko ba kaza ba, ba tare tattara dukkannin bayanan da suka kamata ba, an kuma tantance ingancinsu,” inji Gabkwet.