Masallacin Haramin Ka’aba, Makka
Fassarar Salihu Maqera
Godiya ta tabbata ga Allah, Mai afuwa, Mai gafara, Wanda ni’imarSa ba ta yankewa, kuma Yana karvar tuba daga wanda ya tuba, Ya gafarta wa wanda ya koma gare Shi. Muna gode maSa Maxaukaki godiyar mai miqa wuya da shukura. Muna neman tsari da hasken FuskarSa Mai girma daga kafirci da fajirci. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Mahaliccin sammai bakwai. Kuma na shaida shugabanmu Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa, mai cikakken haske. Ya Ubangiji! Ka qara tsira da aminci a gare shi da alayensa tsarkaka da sahabbansa shugabannin shiriya da waxanda suka biyo su da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, ya ku mutane! Ku bi Ubangijinku da taqawa, ku tuba zuwa gare Shi ta hanyar barin savo zuwa ga xa’a, daga nisantarSa zuwa ga kusantarSa. Ku tuba daga xaudar zunubi zuwa ga tsarkakuwa, domin lallai Allah Yana son masu yawan tuba, kuma Yana son masu tsarkakuwa. Ku sani lallai wajibi ne a tuba daga zunubi cikin gaggawa, ba ya halatta a jinkirta tuba, ko a yi kasala a kanta, domin jinkirta tuba wani zunubi ne da yake buqatar tuba a kan kansa shi ma. Tuba wajiba ce saboda Allah ne Ya yi umarni da ita a cikin LittafinSa, kuma Manzon Allah (SAW) ya yi umarni da ita, ya sanya ta a cikin ayyukan rabo da dacewa a duniya da Lahira. Allah Ya ce, “Kuma ku nemi gafarar Ubangijinku, sannan ku tuba gare Shi, sai Ya jiyar da ku daxi, daxi mai kyau zuwa ga wani lokaci ambatacce, kuma Ya zo wa kowane ma’abucin falala da falalarsa.” Allah Maxaukaki Ya ce, “Ku tuba zuwa ga Allah gaba xaya ya ku Muminai! Tsammaninku za ku samu nasara.” Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ya ku mutane! Ku tuba zuwa ga Allah, kuma ku nemi gafararSa, domin ni haqiqa ina tuba zuwa ga Allah a kowace rana sau xari.” Kuma an karvo daga Abu Huraira (RA) ya ce “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “”Ni ina neman gafarar Allah tare da tuba gare Shi a kowace rana fiye da sau saba’in.” Buhari ya ruwaito shi.
Ya ku Musulmi! Lallai tuba ga Allah wajibi ne, kuma cikin gaggawa, domin umarce-umarcen Allah da na ManzonSa dukkansu ana bin su ne cikin gaggawa, saboda ba a samu dalilin hallacin jinkirta su ba. Kuma jinkirta tuba sababi ne na hauhawa da damfaruwar zunubai su yi tsatsa a kan zukata. Ya zo cikin Hadisi daga Annabi (SAW) cewa, “Idan mumini ya yi wani zunubi sai ya zame masa wani baqin gudan jini a cikin zuciya, idan ya tuba sai a wanke shi daga jikinta, idan ya qara sai ya yi ta girma har sai ya toshe kafar zuciya, to wannan shi ne tsatsar da Allah Ya ambata a cikin LittafinSa. “A’aha! Ba haka ba, abin da suka kasance suna aikatawa dai, ya yi tsatsa a cikin zukatansu.” (Q:83:14).
Ya ku Musulmi! Ku tuba zuwa ga Allah tuba ta gaskiya, sai Allah Ya shafe zunubanku, kuma Ya kankare munanan ayyukanku, Ya xaukaka darajojinku. “Ya ku waxanda suka yi imani! Ku koma (tuba) zuwa ga Allah, komawar gaskiya. Akwai tsammanin Ubangijinku Ya kankare muku miyagun ayyukanku, kuma Ya shigar da ku a cikin gidajen Aljanna, qoramu na gudana daga qarqashinsu a ranar da Allah ba Ya kunyatar da Annabi da waxanda suka yi imani tare da shi. Haskensu yana tafiya a gaba gare su da jihohin damansu, suna cewa, “Ya Ubangijinmu! Ka cika mana haskenmu, kuma Ka yi mana gafara. Lallai Kai a kan dukkan komai, Mai ikon yi ne.” (Q:66:8).
Tuba ba ta kasancewa ta gaskiya, karvavviya, har sai ta haxa sharuxxa biyar:
- Ba za ta kasance karvavviya ba, har sai ta kasance bisa ikhlasi domin Allah, wato ya zama an yi ta, saboda son Allah da girmama Shi da kwaxayin ladarSa da tsoron uqubarSa, ba a yi nufin nuna wa abin halitta ba, kuma ba domin neman wani abin duniya ba.
- Tuba ba za ta zama karvavviya sai mutum ya yi nadama da baqin ciki kan abin da ya aikata na savo, ta yadda zai yi burin ina ma bai aikata savon ba, domin nadamar tana wajabta sadda kai a gaban Allah Maxaukaki da komawa gare Shi.
- Kuma tuba ba za ta zama karvavviya ba, har sai mutum ya ciru daga aikata savo, idan savo ya zamo haram ne ya bar shi a take, idan na barin wajibi ne, ya aikata shi nan take, idan kuma abin da zai iya rama shi ne ya rama. Idan kuma abin da ya shafi haqqoqin bayi ne, ya ciru daga haka, kuma ya mayar musu haqqinsu. Tuba daga giba ba ta inganta alhali mutum yana ci gaba da yin ta. Tuba daga riba ba ta inganta alhali mutum yana ci gaba da mu’amala da ita. Da yawa daga cikin mutane idan aka yi musu nasiha kan su bar aikata savo, sai wani ya ce, “Allah Ya taimake mu mu iya haka.” Madallah da abin da ya faxa, domin in Allah bai taimaki bawa ba, ba zai tsira ba, sai dai kuma wannan kalma ce ta gaskiya da ake nufin qarya da ita, ake nemin uzuri don ci gaba da aikata savo. Wannan kuma ba uzuri ne da aka yarda da shi ba, domin an umarci bawa ya yi aiki nagari ne tare da neman taimakon Allah a kan abin da zai amfane shi. Annabi (SAW) ya ce, “Ka yi yunqurin aikata abin da zai amfane ka, kuma ka nemi taimakon Allah, kuma kada ka nuna gazawa.”
Ba a karvar tubar wanda ya bar yin SAllah a cikin jama’a, alhali yana ci gaba da qin yin Sallar a cikin jama’ar. Ba a karvar tubar mai algushu mai ha’inci, alhali yana ci gaba da aikata su. Duk mai addu’a ko da’awar tuba daga zunubi alhali yana ci gaba da aikata zunubin to tubarsa isgili ne ga Allah. Babu abin da za ta qara masa a wurin Allah sai nisanta, kamar mutum ne ya zo maka yana nadamar yi maka wani abu, amma kuma bai daina ba, haqiqa ba za ka xauki nadamar da yake ba face isgili da raina hankali.
Don haka ku ji tsoron Allah kuma ku bi Allah da taqawa ya ku Musulmi! Ku tuba ga Ubangiji, ku ciru ku bar aikata zunubi.
- Tuba ba za ta zama karvavviya, sai mutum ya yi azama da niyyar ba zai koma ga zunubin ba a nan gaba. Domin idan bai yi azma da niyyar haka ba, to tubarsa ta wani lokaci ne. Da zai samu wata dama zai koma ga zunubi, wato dai tubar muzuru, wadda ba ta nuna cewa ya tuba, saboda ganin munin abin da yake aikatawa.
- Sannan Tuba ba za ta zama karvavviya ba, har sai an yi ta a lokacin da ake karvarta, shi ne lokacin da ke gabanin fitar rai ko fitowar rana ta mafaxarta. Idan ya zamo an tuba a lokacin da ajali ya zo ko rai yake qoqarin fita, ake gargarar mutuwa ba za a karve ta ba. Allah Maxaukaki ya ce, “Bai zamo tuba ba, ga waxanda suke aikata miyagun ayyuka, har sai mutuwa ta halarto wa xayansu, ya ce, na tuba yanzu.” Ma’aiki (SAW) kuma ya ce, “Lallai Allah Yana karvar tubar bawa matuqar bai kai ga gargara ba.”
Idan ya zamo tuba ta zo ne bayan fitowar rana daga mafaxarta ba za a karva ba, saboda faxin Allah Maxaukaki. “A ranar da wasu ayoyin Ubangijnka za su zo, imanin ran da bai yi imani ba a gabani ba zai amfane shi ba, ko kuma bai aikata wani alheri ba a gabani.” Abin da ake nufi da fitar rana daga mafaxarta, shi ne idan mutane suka gan ta tana fitowa daga can suka yi imani gaban xayansu, imanin ba zai amfani rai ba, domin bai yi imani ba a gabani ko kuma bai aikata aikin alheri da imanin ba. An karvo daga Abdullahi bin Amru bin Al’as (RA) cewa Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ba za a gushe ba ana karvar tuba har sai rana ta fito daga mafaxarta, idan ta fito sai a sanya rufi a kan kowace zuciya da abin da yake cikinta.” Ibn Kasir ya ce Hadisin mai kyan isnadi ne. Kuma an karvo daga Abu Huraira (RA) cewa Annabi (SAW) ya ce, “Wanda ya tuba gabanin rana ta fito ta mafaxarta, Allah Zai karvi tubarsa.” Don haka ku tuba zuwa ga Allah Ya ku Musulmi! Ku miqa maSa wuya tare da sallama maSa. Ku haqqaqe cewa tuba ta gaskiya tana shafe abin da ya gabata na zunubbai komai girmansu. Allah Maxaukaki Ya ce, “Ka ce, (Allah Ya ce), “Ya bayiNa waxanda suka yi varna a kan rayukansu! Kada ku yanke qauna daga rahamar Allah. Lallai Allah Yana gafarta zunubai gaba xaya. Lallai Shi, Shi ne Mai gafara Mai jinqai. Kuma ku mayar da al’amari zuwa ga Ubangijinku, kuma ku sallama maSa,a gabanin azaba ta zo muku, sa’annan kuwa ba za a taimake ku ba. Kuma ku bi mafi kyan abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, gabanin azaba ta zo muku, bisa auke, kuma ku ba ku sani ba. (Domin) Kada wani rai ya ce, “Ya nadamata a kan abin da na yi sakaci a cikin sashin Allah, kuma lallai na kasance haqiqa daga masu isgili!. Ko kuma ya ce, “Da Allah Ya shiryar da ni, da na kasance daga masu taqawa. Ko kuma ya ce, a lokacin da yake ganin azaba, “Da lallai za ce ina da wata komawa (zuwa duniya) da na kasance daga masu kyautatawa. Na’am! Lallai ayoyiNa sun je maka, sai ka qaryata game da su, kuma ka yi girman kai, kuma ka kasance daga kafirai.” (Q:39:53-59).
Ya Ubangiji! Ka datar da mu ga tuba ta gaskiya wadda za ta shafe abin da ya gabata na zunubanmu, kuma Ka sauqaqa mana al’amuranmu da ita, Ka xaukaka darajojinmu da ita, lallai Kai Mai yawan kyauta ne Mai girma.
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da Amincin Allah su qara tabbata ga shugabanmu Muhammad da alayensa da sahabbansa baki xaya.