✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jihar Oyo ta samu lafiya -Gwamna Ajimobi

Gwamnan Jihar Oyo Sanata Abiola Ajimobi ya ce gwamnatinsa ta yi rawar gani wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, ta hanyar dakile miyagun…

Gwamnan Jihar Oyo Sanata Abiola Ajimobi ya ce gwamnatinsa ta yi rawar gani wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, ta hanyar dakile miyagun ayyukan gwamnatocin baya. Ya ce yanzu a Jihar Oyo babu sauran rikice-rikicen siyasa da kone-konen kadarori da kashe-kashen rayuka da satar mutane da fashi da makami.

Gwamnan ya fadi haka a lokacin da yake kaddamar da wasu muhimman abubuwa guda 2 da suka shafi tsaro a jihar. Abu na farko da Gwamnan ya kaddamar a ranar Juma’a shi ne, kwamitin amintattu na Asusun Tallafin Tsaro, wanda aka danka alhakin jagorancinsa a hannun Cif Bayo Adelabu, mataimakin Gwamnan Bankin Najeriya. Abu na 2 shi ne yin garambawul ga rundunar hadin gwiwa ta sojoji da ’yan sanda mai suna Operation Burst wacce aka kara mata jami’an tsaro na sojojin ruwa da na sama da jami’an SARS da NSCDC domin ci gaba da ayyukan tsaron lafiyar jama’a a jihar.

Ya ce kaddamar da wadannan muhimman abubuwa guda biyu, babbar nasara ce ga gwamnatinsa wacce ta dakile miyagun ayyuka da gwamnatocin baya suka kasa yin magancewa. A cewarsa, daga 2013 da gwamnati ta kafa Asusun tallafin tsaro da rundunar Operation Burst sai aka yi adabo da miyagun ayyuka a jihar. Saboda haka sai ya nemi wakilan kwamitin da su tabbatar da cewa sun gudanar a ayyukansu kamar yadda doka ta tsara.

Ya kara da cewa, akwai sabon tsarin daukar hotunan talabijin da nadar bayanai da samar da jirgi mai saukar angulu da za a girke su a wasu sassa domin kasancewa cikin aiki a kowane lokaci, ta yadda za a yi maganin miyagun ayyuka a jihar.

 Bayan kaddamarwar ne gwamnan ya yanke kyallen wasu sababbin motoci da kwamitin ya bayar ga rundunar Operation Burst domin gudanar da ayyukan tsaron lafiyar jama’a a Jihar ta Oyo.

Cikin jawabinsa, sabon shugaban kwamitin Cif Bayo ya ce zai yi iya kokari wajen ganin kwamitin ya samu gudunmawar kudi da kayan aiki daga manya da kananan kamfanoni da masana’antu da sanannun attajirai, da za su taimaka wa kwamitin cin ma buri.