Gwamatin Jihar Neja ta ce za ta fara ba ’yan kato-da-gora bindigogi domin su tunkari ’yan bindiga su kuma kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi Jihar.
Gwamna Abubakar Sani Bello ne ya yi alkawarin ne yayin jawabinsa a wani taro da ’yan kato-da-gora sama da 200 a garin Kasuwar Garba na Karamar Hukumar Mariga ta jihar.
- ’Yan bindiga: Rundunar Sojin Kasa ta gargadi Sheikh Gumi kan lafuzansa
- An ci gaba da sauraron shari’ar ‘bidiyon Dala’ na Ganduje
Gwamnan ya bayyana cewa za a ba su makaman ne domin su tunkari mutanen da ya kira makiyan jihar.
Ya ce ziyarar tasa wani salo ne na karfafa musu gwiwa saboda irin rawar da suke takawa wajen yakar matsalar tsaron da yanzu haka ta tasamma zama ruwan dare a jihar.
A baya dai, wasu ’yan bindiga a jihar ta Neja da ma wasu jihohin sun yi kira da a rushe ’yan kato-da-gora a matsayin sharadin da kawai zai sa su ajiye makamansu su rungumi zaman lafiya.
Sai dai Gwamnan ya ce ba za ta sabu ba, sai dai ma a samar wa da dukkan ’yan kato-da-gorar jihar bindigogi domin su samu damar zakulo tare da kakkabe ’yan bindigar a duk inda suke.
Gwamna Sani Bello ya kuma ce babu wata barazana daga ’yan bindigar da za ta sa ya soke ayyukan ’yan kato-da-gora a jiharsa.
“Ba za mu soke su ba saboda barazanar ’yan bindiga. Ko an daina ayyukan ’yan bindiga a nan gaba, wadannan ’yan kato-da-gorar za su ci gaba da samar da tsaro a yankunan kananan hukumominsu,” inji shi.