✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jihar Neja ta gano malamai 5,665 marasa kwarewa a makarantunta

Gwamnatin Jihar Neja ta gano malamai 5,665 da ba su da wata kwarewa ta koyarwa a makarantun firamare da sakandiren jihar. Shugaban Kwamitin tantance malamai …

Gwamnatin Jihar Neja ta gano malamai 5,665 da ba su da wata kwarewa ta koyarwa a makarantun firamare da sakandiren jihar.

Shugaban Kwamitin tantance malamai  jihar, Labaran Garba ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da rahotonsa na wannan shekara ga Gwamna Abubakar Sani Bello a gidan gwamnatin jihar.

Shugaban ya ce, a cikin malaman jihar 24,061 da ke makarantu firamare 3,135, an gano 4,703 ba su da kwarewar da ya kamata su koyar.

Sannan malamai 962 daga cikin 6,870 da ke makarantu sakandare 498 jihar, su ma ba su da kwarewar da ya cancanci su koyar.

Labaran Garba ya kara da cewa ma’aikatan ilimi na kananan hukumomi 1,276 ne ke da cikakkiyar  shaidar ilimin koyarwa.

Daga karshe kwamitin ya bai wa gwamnati shawarar ci gaba gudanar da irin wannan tantance malamai bayan duk shekaru uku, domin samar da ingantaccen tsarin gudanar da harkar ilimi a jihar.

A jawabin gwamnan jihar bayan ya karbi rahoton, yana mai cewa, gwamanati za ta ba kwararrun malamai kulawar da ta kamata, wadanda ba su kware ba kuwa, za’a fitara da su tsarin koyarwa, da kuma ba su zabin su koma su karo ilimi.