Gwamnatin Jihar Katsina na iya kokarinta na ganin ta bude katafaren filin wasan da ta gina mai daukar ‘yan kallo dubu talatin da biyar mai dauke da wajen ajiye motoci akalla dubu uku da dari da dari bakwai.
Daraktan wasanni da motsa jiki na jihar, Alhaji Nalado Kankiya ne ya shaidawa Aminiya haka a ofishinsa da ke Katsina. Ya ce abin da kawai ya rage a cikin aikin filin shi newurin guje-guje da tsalle-tsalle.
Ya ce gwamnatin jihar kakkashin jagorancin Barista Ibrahim Shehu Shema tuni ta kebe wajen motsa jiki na tsofaffi da na masu lalurar hawan jini ko ciwon suga kuma bangaren maza daban na mata daban a filin wasan.
Jihar Katsina ta kusa bude sabon filin wasanta
Gwamnatin Jihar Katsina na iya kokarinta na ganin ta bude katafaren filin wasan da ta gina mai daukar ‘yan kallo dubu talatin da biyar mai…
