Shugaban Kwamitin bincike kan cutar COVID-19 a Jihar Filato, Farfesa Noel Wannang ya ce kwamitin ya yi nasarar gano maganin gargajiya da zai magance cutar.
Ya bayyana hakan ne a Jos a lokacin tattaunawarsa da shuwagabannin kananan hukumomi da masu rike da sarakunan jihar ranar Juma’a.
“Kwamitinmu na bincike ya gano wani maganin gargajiya da zai magance COVID-19 wanda jihar Filato ta zama ta farko da ta cimma wannan nasarar a Najeriya.
“Mun kirkiri magungunan COV PLA-1, COV PLA- 2, COV PLA -3 da kuma PLATABOOST-N.
“Dukkannin itatuwan da aka yi amfani da su wajen hada maganin a jiharmu aka same su. Muna fata za a yi amfani da wannan maganin hatta a kasashen waje da zarar mun kammala binciken”, inji Farfesa Noel.
Ya ci gaba da cewa kwamitin ya kammala zagayen farko na binkice a kan kwayoyin kuma zuwa yanzu sun gano ba shi da wata illa.
“Mun kammala zagaye na farko wanda ya tabbatar cewa kwayoyin ba su da wata illa, kuma za mu fara zagaye na biyu ranar Litinin, 21 ga watan Satumba, wanda daga nan ne za mu fara ba marasa lafiya maganin”, inji shi.
Farfesa Noel ya ce nan ba da jimawa ba za a fara gwajin magungunan a kan lafiyayyun mutane domin tabbatar da tasirinsu, wanda a baya ya ce sun yi amfani da dabbobi kuma magungunan sun yi matukar tasiri a kansu.
Ya ce da zarar an kammal binciken, za a samu sahihin maganin cutar COVID-1, a samar da ayyukan yi sannan a daga darajar jihar a idon masana kimiyya a duniya.
A cewarsa, tuni wasu manyan mujallun binciken hada magunguna irinsu West African Journal of Pharmacy, Pan African Journal of Medicine da ma wasu da dama su ka karbi takardun makalolinsu kuma za su wallafa su nan ba da jimawa ba.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da daidaikun mutane da cibiyoyin bincike ke ikirarin samo maganin cutar a nan Najeriya ba.