✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jigon APC a Adamawa ya gargadi Buhari kan rikice-rikice

Jam’iyyar APC a Jihar Adamawa ta gargadi Shugaban kasa Muhammadu Buhari game da rikice-rikicen da ke aukuwa a kasar inda a cewarta wadansu ne ke…

Jam’iyyar APC a Jihar Adamawa ta gargadi Shugaban kasa Muhammadu Buhari game da rikice-rikicen da ke aukuwa a kasar inda a cewarta wadansu ne ke neman bata wa shugabancinsa suna.

Wani jigo a jam’iyyar, Alhaji  Suleiman Baba Jada ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Yola, inda ya bukaci Shugaba Buhari ya tsananta kan yadda yake tafiyartar da al’amuransa domin akwai wadansu da ke neman bata wa shugabancinsa suna.

Baba Jada ya jinjina wa Shugaba Buhari game da kwangilar hanyoyi da ya ba da wadanda a halin yanzu ana shimfida su sannan ya sake jinjina masa game da daidaita matsalolin tattalin arzikin kasar nan.

Sai kuma ya mayar da martani ga wasikar Obasanjo da kuma furucin Ibrahim Babangida inda a cewarsa, su ne ummul-haba’isin rashawa da cin hanci da kuma tabarbarewar kasar domin son kai.

 “Shugaba Buhari kada ya yi kasa a gwiwa game da maganganun tsofaffin shugabannin kasar Obasanjo da Babangida suke fadi  domin su ne wadanda suka gabatar da rashawa da cin hanci da almundahana a kasar nan,” inji shi.

“A ganina wadannan wasiku sun yi su ne domin son kansu saboda su aibanta shi, don haka Shugaba Buhari ya watsar da kashinsu ya ci gaba da tafiyartar da al’amuransa yadda ya kamata,” inji shi.

Da aka tambaye shi game da mutanen da Buhari ke harka da su amma suna kokarin bata masa suna, ya ce ya kamata Buhari ya dubi lamuran wadannan mutane sosai ya kore su ya nuna musu matsayinsu.

“Ya kamata Shugaba Buhari ya kori munafukan da ke cikin gwamnatinsa saboda irin illar da suke janyo wa gwamnatinsa,” inji shi.

Jada ya kara da cewa sanya Boss Mustapha da aka yi ya maye gurbin  Babachir Lawan a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya ba karamin kuskure ba ne domin akwai kabilu da dama wadanda suka fi su fasaha da hikima.

“Domin kamanta adalci a wannan gwamnatin, Boss Mustapha da aka sa ya maye gurbin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya kuskure ne domin dukansu harshensu daya sannan akwai Kiristoci wadanda suka fi wadannan kabilun iya aiki da kamanta gaskiya a Jihar Adamawa,” inji shi.