✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jigon ɗarikar Tijjaniya, Jauro Bappi, ya rasu a Gombe

Jigon na Tijjaniyya ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya.

Allah Ya yi wa jigo kuma ɗan uwa ga shugaban ƙungiyar Tijjaniya na Afirka, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Alhaji Jauro Bappi, rasuwa.

Alhaji Jauro Bappi yana daga cikin manyan ’yan kasuwar Jihar Gombe da suka jima suna bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar a ɓangarori daban-daban.

Rasuwar Bappi babban rashi ne, ba kawai ga iyalansa ba har ma da mabiya ɗariƙar Tijjaniya da Jihar Gombe da kuma ƙasa baki ɗaya.

Gwamnan jihar, Muhammad Inuwa Yahaya, ya nuna kaɗuwarsa bisa rasuwar ɗan kasuwar.

Gwamnan ya yi ta’aziyya ga iyalan marigayin da mabiya ɗariƙar Tijjaniya, cikin wata sanarwa da Babban Daraktan Yaɗa Labaransa, Isma’ila Uba Misilli, ya fitar a ranar Litinin.

Ya ce ɗarikar Tijjaniya ta yi babban rashi a jihar

Gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan mamacin tare da masa fatan samun Aljanna Firdausi.

Alhaji Jauro Bappi, ya rasu ne sakamakon doguwar jinya da ya yi.

Tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.