Gwamnatin Jahar Jigawa ta yi watsi da filin wasan tseren dawaki na Gumel wanda aka fi sani da Gumel Horse Racing Club sama da shekara uku tun bayan da Gwamna Sule Lamido ya bude kimanin shekaru biyar da suka gabata.
An bar dandalin tseren a wulakance ne al’amari da ya sa karamar Hukumar Gumel ta rika sayarwa mutanen gari da ma’aikatan karamar hukumar ta Gumel wani sashe na filin lamarin da ya sa wasu masu kishi suka sanar da masarautar Gumel halin da ake ciki kuma tuni masarautar ta sanar da gwamnatin jihar halin da ake ciki.
Binciken da wakilinmu ya kalato ya nuna an dauki mataki a kan haka, inda tuni aka hana karamar hukumar sayar da wani bangare na filin. Binciken wakilinmu ya gamno cewa filin yana cikin halin ni ’yasu don hatta rumfar da manyan baki suke zama ta fadi haka abin yake a bangaren da ’yan jaridu suke zama shi ma tuni ya fadi. Bugu da kari babu ruwa babu wuta babu tsaro kai hatta bishiyoyin da ciyayin da aka dasa domin samar da inuwa da baiwa dawakai damar gudu duk sun lalace babu abin da kaka gani sai tumaki da awaki suna kiwo.
Bisa kiyasi an yi asarar dukiya ta sama da Naira miliyan shida da dubu dari shida (N6.7m) lamarin da ya sa mazauna yankin da ke karamar Hukumar Gumel suka dora alhakin watsi da filin a kan gwamnatin Jihar Jigawa.
Jigawa ta yi watsi da filin sukuwar dawaki na Gumel
Gwamnatin Jahar Jigawa ta yi watsi da filin wasan tseren dawaki na Gumel wanda aka fi sani da Gumel Horse Racing Club sama da shekara…