✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jigawa ta kashe fiye da Naira miliyan 4 a yaki da jahilci

Gwamnatin Jahar Jigawa ta kashe Naira Miliyan 4 da dubu 800 wajen sayen kayan aikin koyarwa a daukacin makarantun yaki da jahilci a jihar, inda…

Gwamnatin Jahar Jigawa ta kashe Naira Miliyan 4 da dubu 800 wajen sayen kayan aikin koyarwa a daukacin makarantun yaki da jahilci a jihar, inda kowace karamar hukuma take da makarantu 8 daga cikin kananan hukumomi 27 a jihar.

Sakataren Ilimin Manya, Malam Abbas A. Abbas ne ya shaidawa wakilimmu haka jim kadan bayan kammala rabon kayan da makarantun yaki da jahilci a jahar. Ya ce makarantu 215 suka amfana daga cikin irin kayan karatun da hukumar ta raba, inda makarantun yaki da jahlci matakin farko guda 135 suka amfana da kuma masu mataki na biyu guda 80.

Kayan da aka raba sun hada da allunan rubutu da Alli da littatafan karatu da rubutu da kuma taburmin da ake shinfidawa a cikin ajujuwan karatu. Ya kara da cewar kayan karatun za su taimaka wajen bunkasa harkar koyo da koyarwa a daukacin makarantun kuma wadanda suke yin karatun za su sami kwarin gwiwa wajen dagewa da neman ilimin.