✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jibi za a shawota tsakanin Man United da Arsenal

A jibi Lahadi idan Allah Ya kai mu ne za a kece raini a tsakanin kulob din Manchester United danta Arsenal a gasar firimiyar Ingila. …

A jibi Lahadi idan Allah Ya kai mu ne za a kece raini a tsakanin kulob din Manchester United danta Arsenal a gasar firimiyar Ingila.  Wasan zai gudana ne a filin wasa na Old Trafford wato gidan United kenan da misalin karfe 4:30 na yamma agogon Najeriya.

Wasan zai yi zafi ganin yadda kungiyoyin biyu ke hankoron samun nasara duk da cewa tuni kulob din Manchester City ya lashe kofin firimiyar na bana tun ana saura wasanni biyar a kammala gasar.

Kawo yanzu United ce ke matsayi na biyu a gasar da maki 74 a wasanni 34 yayin da kulob din Arsenal ke matsayi na 6 da maki 57 a wasanni 34.

Ana sa ran gidajen kallon kwallo za su cika makil musamman a Najeriya don ganin yadda wannan wasa zai kaya.

Tuni magoya bayan kungiyoyin biyu suke ta muhawara a kan kungiyar da za ta samu nasara a wasan.

Kocin Manchester United Jose Mourinho da kocin Arsenal Arsene Wenger tuni suka kimtsa don tunkarar wasan da ke daukar hankalin daukacin duniya.