✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Jibi za a rufe gasar

A jibi Lahadi idan Allah Ya kaimu za a rufe gasar cin kofin Afirka da aka fara kimanin makwanni uku da suka wuce a kasar…

A jibi Lahadi idan Allah Ya kaimu za a rufe gasar cin kofin Afirka da aka fara kimanin makwanni uku da suka wuce a kasar Ekuatorial Guinea.

Sai dai da yawa daga cikin masoya kwallon kafa a Najeriya ba su kalli gasar ba, ganin an yi gurmuzun ne ba tare da kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ba.
Binciken da Aminiya ta gudanar ya nuna, mafi yawan masu sha’awar kwallon kafa a Najeriya ba su damu da kallon gasar a akwatin talabijin ba saboda bacin rai na rashin halartar kungiyar Super Eagles gasar. kalilan ne suke zuwa kallon yadda gasar ta gudana a zagayen farko, yayin da wasu kuma ba su fara kallon gasar ba sai da ta kai matakin zagaye na biyu, wasu ma sun ce sai a jibi Lahadi ne suke sa ran za su kalli yadda wasan karshen zai kaya.
kasashe hudu ne dai suka kai matakin semi-fainal da suka hada da mai masaukin baki Ekuatorial Guinea da Kwaddebuwa da Ghana da kuma Dimokuradiyyar Kongo.
Tuni Kwaddebuwa ta kai wasan karshe bayan ta lallasa Dimokuradiyyar Kongo da ci 3-1 a shekaranjiya Laraba yayin da Ghana kuma ta lallas Guinea a jiya Alhamis. Yanzu za a yi wasan karshe ne a tsakanin Kwaddebuwa da Ghana yayin da Ekuatorial Guinea kuma za su kara ne a neman matsayin na uku a gobe Asabar.
Wannan ita ce gasa karo na 30. Idan za a tuna kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles ce ta lashe wadda aka yi a shekarar 2013 a Afirka ta Kudu.