✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jibi Man United za ta kara da Liberpool

A ci gaba da fafatawa a gasar Firimiya ta Ingila karo na 9, a jibi Lahadi ne kulob din Manchester United zai hadu da na…

A ci gaba da fafatawa a gasar Firimiya ta Ingila karo na 9, a jibi Lahadi ne kulob din Manchester United zai hadu da na Liberpool da misalin karfe 4:30 na yamma agogon Najeriya.

Wasan zai gudana ne a filin wasa na Old Trafford wato gidan United.

Kawo yanzu kulob din Liberpool ne yake saman teburin gasar da maki 24 a wasanni 8, lamarin da ke nuna Liberpool bai taba samu rashin nasara ko yin kunnen doki tunda aka fara gasar ta bana.

Sai dai a bangaren United tana matsayi na 12 ne a jerin kungiyoyin da ke fafatawa a gasar, inda ta hada maki 9 kacal a wasanni 8 kuma wannan shi ne kakar wasa mafi muni da United ta fuskanta a shekara 30 da suka gabata.

Masoya harkar kwallo musamman magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta United suna ta rade-radin wannan wasa shi zai tantance matsaytin kocin United, Ole Gunnar Solskjaer don ana ganin idan Liberpool ta doke United to za a kori kocin.