Tsirin tsirfa
Tsefe-tsefen tsifa
Tsokanar tsororuwar tsattsafa
Tsegumin tsugudidin tsufa
Tsangwamar taradaddin tube tufa
Arme
Ararume
An yi kememe
A kai ta kame-kame
An dai yi yayime-yayime
Soki-burutsu
Aura yai tutsu
Karairayin tashin tsuntsu
Laftun labaran mutsu-mutsu
Kanzon kurege ya watsu
Uwargida tai balaguro
An daina jinta a kwararo
Sai aka ce amarsu za a karo
Hira ta karade kowane taro
Wane shu’umi ne ya tunzuro
Burinsu ai ta karo
Baba da Inna su zaburo
’Yan kwaraku an gangaro
Wai za a tamna goriyar goro
Na kishiyar da aka kakaro
Inna ta ce kun makaro
Na riga na juyo
Kowa sai ya kewayo
Ana ta ina ta zagayo
A kashe wutar da aka kyallaro
Jibgin jibar jirga jama’a
Batu ne kamar ba’a
Sai yai ta yaduwa cikin samma’a
Makaryata an gaza ce musu a’a
Wannan karon kiris sui sa’a
Tashen kwaramniyar kwatsam
Kwaran-kwacam
Da kayan kwancam
Kararam
kwankwam
Jijjigar jigata jiki
Juyin jaki
Awarwaron aringizon awaki
Turmutsutsun tunkuyin tumaki
Tururuwar tattaki
Amarsun ango
Doridasonon farin dango
Kankambar karambanin kango
Hange-hangen hayin hango
Gungun gudunmuwar gigiwar gwaggo
Balullubar bulalar Baba
Basajen bugun babba
Barambaramar babatun buba
Yarfen yayimar ayaba
Dumuiniyar dube-duben duba
Aka yi ta zuba zance
Ce-ce-ku-ce
Ka-ce-na-ce
Wane ne ya ce
Zaman zauren zaurance
Kisisinar kishiya
Kai-kawon kulle kucciya
Karatun kumshiya
Kwamraniyar kunkuru da bushiya
Kaudin kaudar kumbiya-kumbiya
Fancalen fincikar falleliya
Ficikar fatalin tsiya
Fankamar fariya
Firgicin fagamniya
Fangimar farfadiya
Mamakon Mama
Ai ta samu dama
Babban bakin ce-ce-ku-ce
Ya jiwo abin da ta ce
Lumar uwarjiki ce makama
Watan Akwatun-Babba ya kasance dibge da mukun-mukun makonnin makarkashiyar mamayar Mama mai makekiyar makarantar mutunta mutane, inda aka yi mata tashin-tashinar tashen KWARAN-KWACAM DA KAYAN KWANCAM, HAKURI YAYA. An dai tsiwurwurta wannan ta’asa ce sanadiyyar tsawon lokacin da aka dauka ba a ji duriyarta ba a fadar Tsaunin Bila da kafafen yada kwakwazo na kasar Haurobiya suka yi.
Kai wadansu da suka zarta gayauna da irin shuke-shuken dashe-dashe, har ma bazawa suka rika yi cewa, an shirya bikin ajo da kade-kaden taka rawar banjo, wai za a kawo wa Mama kishiyar hajijiyar Hajo, Uwa-uba ma wadansu masu tsokane-tsokanen tsangwamar tsugudidin tsegumi, har tururuwa suka yi a mafuskantar alkibla da ke fadar mulki ta Tsaunin Bila, don yi wa ango da amarya du’a’in zaman lumana, in ma an raba goriyar goro su dan samu su tauna. Domin ta haka ne za su tabbatar da cewa su ganau ne, ba jiyau ba.
Tuni dai da na ji wannan ruwaya marar inganci, cike da ganganci, sai kawai na dauke ta a matsayin shashanci, duk da cewa na ga takardar gayyata da aka baza a shafukan fuskantar-bokoko da tukin tuwon titi da watso-watson-zufa, wato dai kafatanin kaftun kofaton kafofin karambanin kambama yarfen yari-yarin yadon yadiya da suka haifar da JIBGIN JIBAR JITA-JITAR JIRGA JAMA’A.
Daukacin wannan lamari da ya auku ga mai dakin Baban-burin-huriyya, babban darasi ne ga mahukunta cewa, ana bin kadin wainar da suke toyawa a farfajiyar fadar mulki. Kuma lallai a makekiyar makarantar Mama a rika yin darussan daidaita dumuiniyar dagar amarsun alkinta aikin agogon ango, don kada a yi mana: Auratayyar amaren arme kememe ai ta rarume-rarume, ana ta kame-kame da yayime-yayime. Kodayake dai wani hanzari ba rarewa a runtuma a guje ba, ta yiwu BALULLUBAR BULALAR BABA ce ko BASAJEN BUGUN BABBA, wadda ta kacame, ta zamo baram-baramar babatun Buba, a salon yarfen yadon yadiyar yayimar ayabar dumuiniyar dube-duben duba.
’Yan makaranta a yi karatun ta-natsu, gudun kada a karke da tsuwwa tsu-tsu ko fuffukar falle fuka-fukin tsuntsu; idan kuwa aka ci kasa, ana iya karkewa da jan cikin tsayuwar tsutsa. Domin irin hakan na iya haifar da jijjigar jigata jikin juyin jaki a dabaibayin awarwaron aringizon awaki da turmutsutsun tunkuyin tumakin tururuwar tattakin take-taken tabarbarewa.
Batu na ingarman karfen karafan karfa-karfa da dai wannan jibgin jibar jita-jitar jirgata jama’a, ai gara a ce an yi gangankon gangamin gamayyar gyaran girar gararumar gara, ta yadda za a kakaba wa ’yan matan jaba da gafiya da samarin-kusu sasarin sihirin susucewa. Yin hakan ya zama dole, domin a ranar nazarin ingancin kwakwalwa ta duniya an baje jidalin jadawalin jimurdar juyewar kwanyar dimbin Haurobiyawa, musamman masu jikkata kurungunsu da haramben handame haramiyar hallaka halaliyarsu.
Wannan na nufin da batu aka ce an baza kan KIDAN KOKON DUHUND-UNDUMDURUNDUM ko TSAWWALAR TSURKUN TSUKUKUN TSUKEWAR TSAKA-MAI-WUYA ba lallai ne su yi wani tasiri ba, tunda ’yan gyare-gyare irin na gyare da kurege ake bukata kawai, ta yadda za a yi ta kwasar gararumar gwagwabar gara.
Kai kamata ya yi ma a baza jita-jita bazo-bazo cewa, “Gwamnatin Baban-burin-huriyya za ta yi wa talakawan kasar nan BELIN-AUTA,” musamman ma ganin bayan da ta garkame gingimemen gambun kan iyaka, masu fama da talalar talauci ke kara jigata. Domin kowane irin alfanu wannan na-mijin yunkuri ke tattare da shi, musamman wajen hana safarar kayan mamaye kwakwalwa da miyagun makamai, marasa galihu dai ke ta kara jin jiki. Kai a dai ci gaba da gashi, suya kuwa sai Ranar Sallah, ta yadda idan an samu salala, an hana wasu arcewa da sulalla, to babu wanda zai ji a salansa. Kun ga ke nan akwai yiwuwar ko dai mu daina marmarin samfarerar samfurin kasar Tayar-Landan, ko kuma mu ci gaba JIMIRIN JINKIRIN JAN-KARIN JIRAN JIMBIRI!
Kai ni ma ga jibgin jita-jitar jijjiga jama’a nan zan cillo, wato: a akwatun magana mai jini na yi kasake, na jiwo, wai BABA ZAI KWACE LASISIN KIDAN KOKON DUHUNDUNDUM DURUNDUM: DAMIN MATSABBAN DA IRO MUGUN MADAMBACI YA KWATO ZA A JINKA WA TALAKAWAN HAUROBIYA A MATSAYIN BELIN-AUTA; sannan kadarorin Samarin-kusu da ’yan matan jaba da gafiya za a cefanar da su, a dan raba wa kowa da kowa a kasar nan.
Duk za a gudanar da wannan namijin kokari ne da zimmar kawo karshen HALIN-BURTU: A BADDA KAMA, A YI BARNA! Tirkashi!
Bisa la’akari da turka-turkar tufkar da aka tafka, sai mu ce Haurobiyawan da suka baza jibgin jibar jita-jitar jirga jama’a, ba su kyauta wa al’umma ba. Domin ko an kama uwargida da tu’annatin tunkude KISISINAR KISSAR KASSARA KISHIYA, ai masu hakki na iya bin kadin hakkinsu. To ina ruwan biri da gada. Haka nan a banzar bazara kun cika mu da surutu rututu kamar Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ratatata!