✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jesse Lingard ya raba gari da Manchester United

Kungiyoyi da dama sun shiga zawarcin dan wasan

Manchester United ta sake fitar da sanarwar raba gari da dan wasanta, Jesse Lingard, bayan kwantaraginsa ya kare da kungiyar.

Lingard, wanda ya shafe kakar wasanni ta bara a kungiyar kwallon kafa ta West Ham a matsayin aro dai ya gaza katabus a Manchester United a bana.

Dan wasan wanda dan asalin Ingila ne ya bi sahun Paul Pogba, na jerin ‘yan wasan da suka yi sallama da kungiyar.

Sanarwar ta ce “Manchester United ta tabbatar da Jesse Lingard zai bar kungiyar a karshen watan Yuni, idan kwantaraginsa ya kare.

“Muna amfani da wannan dama don gode wa Jesse kan yadda ya taimaki wannan kungiya a lokacin zamansa, muna masa fatan alheri a rayuwarsa ta gaba.”

A watan Janairu, Newcastle ta nuna sha’awar daukar dan wasan tsakiyar, amma Manchester United ta yi burus da tayin nata.

Kazalika, kungiyoyi kamar su AC Milan, Inter Milan, Juventus da kuma Atletico Madrid daga gasar Laliga sun nuna sha’awar daukar Jesse.