✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Jese kuma ya koma PSG

Jese Rodriguez dan kwallon gaba a kulob din Real Madrid da ke Sifen ya samu nasarar canza sheka zuwa kulob din PSG da ke Faransa…

Jese Rodriguez dan kwallon gaba a kulob din Real Madrid da ke Sifen ya samu nasarar canza sheka zuwa kulob din PSG da ke Faransa a tsawon kwantaragin shekara biyar.
A ranar Litinin da ta gabata ne kulob din PSG ya tabbatar da canza shekar dan kwallon zuwa Faransa akan Fam miliyan 25 kwatankwacin Naira biliyan 12 da miliyan 625. Ya buga wa kulob din Madrid wasa sau 38 a bara inda ya samu nasarar zura kwallaye 6 a raga.
Komawar da dan kwallon Jubentus na Italiya Albaro Morata zuwa Madrid na daga cikin dalilin da ya sa Jese ya yanke shawarar barin Madrid don ya san da wuya ya rika buga wasa a kan kari.