Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin sabbin hadimai da mashawarta 18 da za su jibinci lamuran ayyukan Gwamnatin Tarayya a matakai daban-daban.
Babban Daraktan Yada Labarai a Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Mista Olusola Abiola ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja.
- Majalisar Kano za ta karrama matashin da ya dawo da N15m da ya tsinta
- Tinubu ya isa New York don halartar taron Majalisar Dinkin Duniya
A cewar Mista Abiola, tawagar sabbin hadiman ta kunshi mashawarta na musamman 6 da kuma manyan hadimai na musamman 12 da za su yi aiki a karkashin Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima.
Ya bayyana sunayen wadanda aka naɗa da suka haɗa da Rukayya El-Rufai a matsayin bai da shawara ta musamman kan Majalisar Tattalin Arzikin Kasa (NEC) da sauyin yanayi da Tope Kolade Fasua, mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin tattalin arziki.
Ya ce an nada Aliyu Modibbo a matsayin mai ba da shawara na musamman kan ayyuka; Hakeem Baba-Ahmed, mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa; da Jumoke Oduwole, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan Hukumar Kula da Harkokin Kasuwanci da Zuba Jari ta Kasa (PEBEC).
Abiola ya ce, sauran sun hada da Sadiq Wanka, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan samar da wutar lantarki da Usman Mohammed, babban hadimi na musamman ga shugaban kasa kan harkokin mulki da daidaita ofisoshi da Kingsley Nkwocha, babban hadimi na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da sadarwa.
Haka zalika, an nada Ishaq Ningi, babban hadimi na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai na zamani da bayar da agajin gaggawa da Peju Adebajo, babban hadimi na musamman ga shugaban kasa kan harkokin zuba jari da kamfanoni da Mohammed Bulama, babban hadimi na musamman ga shugaban kasa kan harkokin siyasa da ayyuka na musamman.
Hakazalika, Abiola ya ce Mista Kingsley Uzoma shi ne babban hadimi na musamman ga shugaban kasa kan harkokin noma da inganta ayyukan noma da Gimba Kakanda, babban hadimi na musamman ga shugaban kasa kan bincike da nazari.
Abiola ya kuma ce Temitola Adekunle-Johnson shi ne babban hadimi na musamman ga shugaban kasa kan samar da ayyuka da kuma masana’antu da Nasir Yammama, babban hadimi na musamman ga shugaban kasa kan kere-kere; sai kuma Zainab Yunusa ita ce babbar hadimar shugaban kasa kan Majalisar Tattalin Arziki.
Sauran su ne Mariam Temitope, babbar hadima ta musamman ga shugaban kasa kan shirye-shiryen raya yanki, da Bashir Maidugu, babban hadimin shugaban kasa kan sha’anin shawara a Fadar Gwamnati.