✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisar Kano za ta karrama matashin da ya dawo da N15m da ya tsinta

Majalisar ta ce za ta tallafa wa matashin kan nuna hali nagari da ya yi.

’Yan majalisar dokokin Jihar Kano sun yi alkawarin bayar da wani kaso daga cikin albashinsu ga matashin nan mai Adaidaita Sahu da ya dawo da Naira miliyan 15 da ya tsinta.

Hakan dai ya biyo bayan kudirin bayanin da dan majalisa mai wakiltar mazabar Doguwa, Alhaji Salisu Muhammad ya gabatar a yayin zaman majalisar wanda Alhaji Isma’il Jibril Falgore ya jagoranta.

Aminiya ta ruwaito yadda matashin mai suna Auwalu Salisu dan shekara 22 ya mayar wa mai kasar Chadi zunzurutun kudi har Naira miliyan 15 da ya manta a babur dinsa.

A zaman majalisar, Muhammad ya kafa hujjar cewa direban babur din ya nuna aminci ta hanyar mayar da kudaden da suka bace duk da halin da iyalinsa ke ciki da kuma halin matsin tattalin arziki da ake fuskanta.

Da yake mayar da martani, Falgore ya yi nuni da cewa majalisar za ta gayyaci matashin don bayar da gudunmawar su.

’Yan majalisar 40 da ke wakiltar kananan hukumomi 44 na Kano sun goyi bayan wannan kudiri tare da yin alkawarin mara wa matashin baya don zaburar da shi tare da yin kira ga sauran jama’a da su yi koyi da kyawawan halayensa.