✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jerin sunayen iyalan Sarkin Kajuru da ke hannun ’yan bindiga

Har yanzu akwai mutum 13 da ke tsare a hannun ’yan bindigar.

Duk da an yi farin cikin dawowarsa, har yanzu sauran mutanen da ’yan bindiga suka sace tare da Sarkin Kajuru, Alhaji Alhassan Adam suna tsare.

Cikin kasa da sa’a 24 da sace shi, Sarkin Kajuru ya shaki iskar ’yanci bayan da bayanai suka tabbatar cewa ’yan bindigar da suka yi awon gaba da shi sun sako shi.

A yammacin ranar Litinin ce jama’ar gari suka cuncirindo wajen yi wa sarkin lale maraba da dawowa.

Majiyar rahoton ta ce har yanzu ba a sako sauran mutum 13 da aka sace tare da Sarkin ba.

A Lahadin da ta gabata ce ’yan bindiga suka kai hari garin Kajuru da ke Jihar Kaduna, inda suka sace Sarki da wasu mutum 13 cikin har da iyalansa.

Ga jerin sunayen wadanda har yanzu ke tsare a hannun ’yan bindigar:

 • Zainab Alhassan (Diyarsa)
 • Zainab Mukhtar (Jikanya)
 • Muhammad Sa’adanu  (Jika)
 • Salim Musa  (Jika)
 • Faisal Musa  (Jika)
 • Ahmed Mukhtar  (Jika)
 • Suleiman Umar (Wani basarake a Kajuru)
 • Nazifi Rayyanu
 • Ayuba Yunusa
 • Amina Abubakar
 • Maryam Abubakar
 • Mardiyya Sani
 • Mudassir Sani