✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jerin hare-haren da suka auku cikin mako daya a Abuja

Tun bayan harin Gidan Yarin Kuje ake zaman dar-dar a Abuja.

Matsalar tsaro a Najeriya na daga cikin manyan kalubalen da suka dabaibaye kasar nan, inda ‘yan bindiga da barayin daji ke ci gaba da addabar sassa daban-daban ta hanyar kai hare-hare da sace-sacen mutane musamman a Arewacin Najeriya.

Matsalar ta yi karfin da hatta Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Sha’anin Tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya, ya fito ya ce ’yan Najeriya sun gaji sun kuma fara tunanin daukar matakan kare kansu da kansu.

Abuja da ke zaman babban birnin tarayyar kasar da ake ganin ya fi ko’ina tsaro a fadin kasar, shi ma bai tsira ba, domin a baya-bayan an samu aukuwar jerin hare-haren da ‘yan bindigar suka kai a sassan birnin.

Aminiya ta yi nazari tare da kalato hare-haren da suka auku a sassan Abuja a tsakanin ‘yan kwanakin da suka gabata kamar haka:

Masu Gadin Fadar Shugaban Kasa

A ranar Juma’a, 22 ga Yuli, mahara suka kai wa dakarun Bataliya ta 7 ta Sojojin Najeriya, wadanda ke gadin Fadar Shugaban Kasa hari.

Harin ya auku ne cikin daren wannan rana a yankin Bwari, wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojoji takwas tare da jikkata uku.

Bayanai sun ce babbar manufar maharan ita ce kai wa makarantar sanin makamar aikin lauya (Nigerian Law School) da ke Bwari hari.

Hanyar Kubwa-Bwari

Sai kuma harin da aka kai da daren ranar Litinin, 25 ga Yuli, inda ‘yan ta’adda suka sake yi wa dakarun da ke gadin Fadar Shugaban Kasa kwanton-bauna sa’ilin da suke sintiri a kan hanyar Kubwa zuwa Bwari.

Mai magana da yawun rundunar dakarun, Kyaftin Godfrey Anebi Abakpa, ya tabbatar da faruwar haka.

Kodayake dai, ya ce dakarun nasu sun yi nasarar dakile harin.

Kauyen Sheda

‘Yan bindiga sun kuma kai hari a Lahadin da ta gabata a kauyen Sheda da ke yankin Kwali a birnin na Abuja, inda suka sace wani magidanci, Mista Sunday Odoma Ojarume da matarsa Janet Odoma Ojarume.

Sai dai an sako matar daga bisani.

Shingen Kusa Da Tsaunin Zuma

Sai kuma harin baya-bayan nan da ‘yan bindigar suka kai wa sojojin da ke bakin aiki.

An kai wa sojojin hari ne a shingen bincike ababen hawa a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, kusa da Tsaunin Zuma a ranar Alhamis da ta gabata.

Harin da ya yi sanadiyar mutuwar akalla soja daya.

Haren-haren da Abuja ta fuskanta a tsakanin ‘yan kwanakin nan, ya yi sanadiyar rufe makarantu a birnin don kare rayukan dalibai da na malamansu.

Tun bayan harin da ‘yan bindiga suka kai Gidan Gyaran Hali na Kuje, wanda ya yi sanadiyar tserewar wasu fursunoni ciki har da mayakan Boko Haram, ake zaman dar-dar a birnin na Abuja da kewaye.